Da Dumi Dumi

Katsina: Masu garkuwa sun sako mutum 11 za a sako 18 yau

Gwamnatin Katsina ta ce, ta karbi mutum 11 da masu garkuwa da mutane suka kama, a yau ana saran za a sake sako karin wasu mutum 18 da suke hannnun su sakamakon sasantawar da aka yi tsakanin su da gwamnatin jihar lokacin da ‘yan bindigar suka sanar da aje makamansu.

Tun a ranar Lahadi ‘yan bindigar suka fara sako mutum biyar daga bisani suka sako mutum shida.

Gwamnan jihar Katsina Aminu Masari, ya ce an sako wadanda aka kama ne sakamakon yarjejeniyar da aka yi da ‘yan bindigar kuma ya kara da cewa, ba a biya kudin fans aba kafin a sako wadanda aka kama.

Share