✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Katsina Max Air ya lashe babban kofin gasar Polo ta Katsina

A ranar Asabar da ta gabata ne aka kammala gasar wasan kwallon dawaki na shekara-shekara a Katsina inda kulob din Katsina Mad Air na Lawal…

Wasu daga cikin ‘yan kwallon dawakin da suka fafata a gasar Max AirA ranar Asabar da ta gabata ne aka kammala gasar wasan kwallon dawaki na shekara-shekara a Katsina inda kulob din Katsina Mad Air na Lawal Mangal ya lallasa na Abuja Rubicon na Sanata Hadi Sirika da ci 11 da 10 a gasar cin kofin Najeriya, kofin da ya fi girma a gasar.
Ita dai wannan fafatawa an yi tane har kashi uku a tsakanin wadannan kungiyoyi biyu bayan janyewar da kulob din Kaduna Profile a gasar.
An yi karawar farko a tsakanin Katsina Mad Air da Abuja Rubicon inda aka tashi Mad Air na da kwallaye 9 yayin da Rubicon ke da 6 a Chukka 4 daga cikin 5 da ake bugawa akan wannan kofi inda aka rabu a haka saboda kurewar lokaci.
An dawo ranar Asabar ranar da ake kammala wasan inda aka buga Chukka daya da ta yi kwantai inda Abuja Rubicon ta samu nasarar saka kwallaye 4 a ragar Mad Air kuma aka tashi (10-9). Bayan cika ramakon da aka yi ne aka sake fitowa a karo na 2 don sake buga wata Chukkar 5 don fitar da gwani kamar yadda tsarin wasan yake. Anan ne Lawal Mangal da Umar Kabir da Muhammadu Usman Sarki tare da Farnando Bourdie dan kasar Ajantina na Katsina Mad Air suka cewa su Sanata Hadi Sirika wanda kuma shi ne mataimakin shugaban hukumar kwallon dawaki ta Najeriya watau “Nigeria Polo Federation (NFP) na daya tare da Abdulmalik Badamasi da Idris Badamasi da Jamilu Mohammed na Abuja Rubicon cewa ruwa ba tsaran kwando ba ne a inda Mohammadu Sarki ya fara saka kwallo a raga bayan Farnando da Umar sun gyara masa. kwallo ta biyu kyaftin na Tim din Lawal Mangal ne ya saka ta a ragar Rubicon a Chukka 5 da aka buga a karo na biyu wanda ya ba Mad Air damar cinye gasar da kwallaye 11 yayin da Rubicon suke da 10.
A gasar cin Kofin Janar Hassan kuma wanda yake shi ne kofi na biyu mafi girma a gasar, Katsina Masanawa ne ta hannun matasan ‘yan wasa irin su Ibrahim U. Sarki ne suka lashe shi. Kofin Talba na uku a gasar, Abuja Guard ASI ne suka lashe shi yayin da kofi na hudu a gasar, Katsina danmarina ne suka lashe.
An dai buga wasannin na tsawon mako daya ne a tsakanin filayen wasan kwallon dawakin biyu da ake da su a Katsina watau filin wasa na tunawa da Sarkin Katsina Usman Nagogo wanda yake mutum na farko a Najeriya da ya kai matsayin mai +7 a wasan Polo, sai kuma filin wasa na kan hanyar Jibiya wanda aka fi sani da gonar Dikko Ladan. An dai samu wadannan sauye-sauyen wajen wasa ne saboda an gudanar da wasan a cikin tsakiyar damina domin baiwa filayen samun tsanewar ruwan da kan kwanta a ciki.
Gasar ta samu bakuncin Kwamishinan Matasa da wasanni na Jahar Katsina, Alhaji Mannir Talba wanda ya wakilci Gwamnan Jaha Barista Ibrahim Shehu Shema da Mai Martaba Sarkin Daura Alhaji Farouk Umar Farouk, wanda kuma bisa al’ada yake bayar da kyautar sandar wasa ga dan wasan da ya fi nuna kwazo sai Mai Martaba Sarkin Maru na Jahar Zamfara Alhaji Abubakar Chika Ibrahim tare da mai masaukinsu Mai Martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmuminu Kabir.
An rarraba kyaututtuka ga ‘yan wasa ta fannoni daban-daban ciki kuwa har da ta dan wasan da ya fi kowa ladabi wadda Hassan Shema ya samu.
Tun farkon wasan har zuwa karshensa ba a samu wani mummunan hadari ba sai dai dan abin da ba a rasa ba.