Da Dumi Dumi

Kauyen da mutane ke shan ruwa tare da dabbobi

Kududdufin Unguwar Mangwaro
Yaran kauyen Gayan ko Unguwar MMangwaro suna diban ruwa a kududdufin bayan gari

Da zarar gari ya waye a kauyen Gayan ko Unguwar Mangwaro, kamar yadda aka fi sanin shi, da ke gundumar Jagindi a karamar hukumar Jama’a ta Jihar Kaduna, daya daga cikin abubuwan da yara ke fara yi shi ne debo ruwa.

Sai dai kuma a kauyen kaf babu inda za su ruwan da za su sha ko su yi wanki ko wanka, don haka sai dai su tafi bayan gari.

A bayan garin ne kududdufin da suke diban ruwa yake – a kududdufin da makiyayan da ke makwabtaka da su ke koro dabbobi su shayar da su.

Wani mazaunin garin mai wa’azin Kirista, Christopher Cindo, ya ce rashin daya ne daga cikin kalubalen da kauyen ke fuskanta.

“Ba mu da ko rijiyar burtsatse da gwamnati ko wasu qungiyoyi suka haqa, kuma duk lokacin da muka haqa rijiya ba ma samun ruwa. Hakan ya sa dole muke shan ruwan kududdufin,” inji shi.

ADVERTISEMENT

Shi ma Yusuf Adamu mazaunin garin ne, ya kuma ce yaransu na fuskantar matsalar rashin lafiya sanadiyyar ruwan kududdufin da suke sha, inda ya ce idan ba ’ya’yansu sun yi tafiya zuwa wani gari ba ne to ba su taba dandana ruwan famfo ba.

Don ilimin yaran dai akwai makarantar firamare daya mai aji uku wadda aka shaida wa Aminiya cewa mutanen garin ne suka gina da kansu, sai karin aji biyu da ofishi daya da aka ce an gina musu ne.

Bayan wannan kalubale, wani bangare da ke haddasa wa mutanen kauyen ciwon kai shi ne kiwon lafiya.

A cewar Mista Cindo, sukan yi tafiyar kilomita tara kafin su je wani karamin asibiti a wani gari mai suna Unguwar Yuli.

Bayan wannan kuma, sai matsalar yadda za su yi da amfanin gonarsu, tun da su manoma ne; a cewarsa sai sun hau kwale-kwale sun ketare rafi kafin su je garin Jagindi, inda suke sayar da abin da suka noma sannan su sayo kayan bukata na yau da kullum.

“Wannan hanya da ake ketare rafi ita ce wacce ta fi sauki domin tafiyar kilomita hudu za ta kai mu Jagindi, sai dai matsalarta da damina muna shan wahala.

“Idan muka bi ta daya hanyar kuwa akalla sai mun shafe wajen kilomita 14 kafin mu kai Jagindi saboda babu hanya mai kyau,” inji shi.

Dagacin garin, Adamu Bawa, bayan tabbatar da abin da mutanen suka zayyana wa Aminiya, ya kara da kokawa da yadda aka dauke musu akwatin mazabarsu aka kai shi wani waje nesa da su.

Ya ce bai san abin da ya sa aka dauke musu akwatin jefa kuri’arsu ba alhali suna da yawa.

“Kuma wannan ruwan da kake gani bayan mun debo ne sai mu ware wanda za mu sha, mu dafa ko mu sanya alumu a ciki, hakan ne muke samun sauki kadan da ba mu san irin cututtukan da za mu sha ba.

“Mu dai Allah kawai Ya ke kare mu,” inji shi.

Dagacin ya ce suna zaune lafiya Musulmansu da Kiristocinsu domin dukkansu kabila guda ce ta Gwandara.

Wani magidanci kuwa kokawa ya yi da matsalar rashin ilimin addinin Musulunci da ’ya’yansu ke fuskanta duk da kasancewar uku bisa biyar na mutanen garin Musulmi ne, inda ya yi kira ga jama’ar Musulmi su taimaka ko ta hanyar zuwa ne ana karantar da ’ya’yansu addini.

“Ga mu da yara da yawa amma babu makarantar Islamiyya ko daya kuma babu wani malami da ke zuwa don karantar da su sai dai ranar Juma’a da wani malami ke zuwa daga garin Jagindi don yi mana Sallar Juma’a,” inji shi.

Sun roqi hukumomin da abin ya shafa su taimaka musu da hanyar mota da gada da dakin shan magani da ruwan sha mai tsafta.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya