Da Dumi Dumi

Kawo karshen rigingimun Fulani makiyaya da manoma na hannun gwamnonin Arewa

Tunda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya hau karagar mulki a shekarar 2015, daya daga cikin matsalolin da ya gada kuma ya nuna himmar zai kawo karshensu ita ce matsalar rigingimun Fulani makiyaya da manoma.Wadda zuwa wannan lokaci a kullum take daukar sabon salo irin na ta’addanci da a da ba a san da shi a cikin wannan rigima ta shekaru aru-aru ba. Duk wani dan Arewa ya taso ya ji ko ya ga yadda akan samu fadace-fadace a tsakanin Fulani makiyaya da manoman jihohin Arewa, duk lokacin da aka ce an fara girbin amfanin gona, lokacin da Fulani makiyaya kan danno daga Arewacin Arewa (wadasunsu ma ana zargin daga kasashen makwabta suke), zuwa Arewar.

A da can lokacin kadai aka sa ni ana samun irin wadancan rigingimu da akan zubar da jini da asarar rayuka da dabbobi da amfanin gona.

Amma a ’yan shekarun nan (shigowar wannan jamhuriyya), fadace-fadace da zubar da jini da kashe-kashe a kullum sai dada fadada da munana suke yi, ta yadda a kwanakin baya a wani rahotan da ta fitar a ranar 10 ga Yunin da ya gabata, Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Kasa da Kasa ta  Human Rights Watch (HRW), ta bayyana cewa daga shekarar 2015 zuwa wancan lokaci fiye da mutum dubu 3 da 641 suka mutu a rikici da fadace-fadacen Fulani makiyaya da manoma a kasar nan.

Rahoton ya kara da cewa a cikin wata shida na  bana, wato Janairu zuwa Yuni ’yan ta’adda a Jihar Zamfara sun kashe mutum 262. Sannan yanzu maganar da ake yi jihohi 12 da suka hada da Kano da Legas da Yobe da Abiya da Jigawa da Bayelsa da Bauchi da Ribas da Gombe da Kuros Ribas da Osun da Akwa Ibom ne kadai ba ka jin ana kokawa da ta’addancin da ake jinginawa ga Fulani makiyaya. Su ma din za ka tarar suna fama da matsalolin rashin tsaro irin na garkuwa da mutane don neman kudin fansa da makamantansu da suka game kasa. Amma sauran jihohi 24 da Babban Birnin Tarayya Abuja, suna fama da ta’addanci da fitinu irin na Fulani makiyaya da manoma da sauransu.

Don kawo karshen wannan annoba ta rikicin Fulani makiya da manoma ya sanya a shekarar 2015, gwamnatin Shugaba Buhari ta fara lalubo bakin zaren, wanda da farko ta ce za ta bullo da sabon tsarin yin kiwo ga Fulani makiyaya a wuri-wuri a dukkan jihohin kasar nan, ta hanyar tadanar wa makiyaya wuraren yin kiwo da ke dauke da ciyawa da dam-dam, ta yadda za ta takaita yawon kiwonsu, amma sai wasu gwamnonin jihohi, musamman na Arewa ta Tsakiya da Kudancin kasar nan suka yi watsi da ita.

ADVERTISEMENT

A shekarar 2016, Gwamnatin Tarayyar ta sake yunkurowa da nufin tsungunar da Fulani makiyayan, nan ma wadancan gwamnonin jihohi suka ce ba ta sabuwa wai bindiga a ruwa. Kamar wasan kwaikwayo a bara, gwamnatin Buhari ta sake bullo da tsarin kafa wa Fulani makiyaya sansanin dabbobi, shi din ma ala dole ta fasa, bisa ga kin amincewar wadancan gwamnoni da wasu daga cikin mutanensu.

A bana  ma Gwamnati Tarayya ta kwata, bisa ga damuwar da ta yi a kan yadda rikicin Fulani makiyaya da manoma da sauran al’ummar kasa ya zama annoba, don haka ta ce za ta kafa Rugage a fadin kasar nan, shirin bisa ga yadda aka dade ana son kawo karshen matsalolin, har an samu jihohi 12  dukkansu daga Arewa da suka ce sun amince da shirin kafa RUGAR, amma ala tilas bisa ga bijirewa da wadancan gwamnoni suke kai da wadansu daga cikin mutanensu ya sa Gwamnatin Tarayyar ta sake ba da shelar ta dakatar da shirin RUGAR, har sai ta samo wasu hanyoyin da za su zama dan kallo lafiya mai wasa lafiya.

Mai karatu ya kamata ka gane cewa dukkan wadancan shirye-shirye da Gwamnatin Tarayya ta yi hobbasar yi manufarsu daya ce, wato yadda za a samu a rika samar wa Fulani makiyaya kula ta musamman ga su kansu da ’ya’yansu da dabbobinsu. Ma’ana wuraren kiwo da mashaya da fannin ilimi da na lafiya da na habakar tattalin arzikin su kansu Fulani makiyayan da ’ya’yansu da dabbobinsu, abubuwan da za su amfani duk wani dan kasar nan idan sun kankama. Amma saboda raini da rashin amince wa juna da kiyayya irin ta bambancin addini da kabila da yadda wadansu masu ruwa-da-tsaki kan yadda za a samu nasarar kawo karshen rikice-rikicen suke amfana da ci gaba da ruruwar wutar rikicin wajen samun biyan tasu bukatar da uwa-uba yadda wadansu gwamnoni suke ganin za a kwace filayen mutanensu a ba baki, suna daga cikin abubuwan da suke ta kara jagwalgwala batun, ta yadda ake kallon al’amarin tamkar babu mafita.

Har an kai fagen da gwamnonin jihohin Kudu da kungiyoyin kabilunsu, sun kai matakn ba Fulani makiyaya da ke jihohin umarnin su  hanzarta ficewa daga jihohinsu, su san inda dare ya yi musu.

Daga Arewa wadansu daga cikin kungiyoyin yankin  sun mayar da martani sun ba musamman ’yan kabilar Ibo da ke zaune a Arewa umarnin su hamzarta komawa jihohinsu.  Wata kungiyar kuma cewa ta yi lallai idan har gwamnoni da sauran mutanen jihohin Kudu ba sa son zaman Fulani makiyaya a jihohinsu, to, Fulanin su gaggauta baro masu yankunansu.

Shi kuwa Shugaba Buhari cewa ya yi koda wai kada Fulani makiyaya su kuskura su baro jihohin Kudu, yana mai cewa Kundin Tsarin Mulkin kasar nan ya sahale wa kowane dan kasa ya sakata ya wala a duk inda yake bukata a cikin kasar nan

Yanzu maganar da ake an sake jin Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje yana maimaita hirar da ya yi da Sashen Hausa na Radiyon BBC, Landan, a Sakkwato Birnin Shehu a karshen makon jiya, inda yake shawartar Gwamnatin Tarayya ta hana Fulani makiyaya tafiya kiwo zuwa tsakiya da kudancin kasar nan, abin da ya ce shi ne kadai da zai taimaka wa rayuwar Fulanin da dabbobinsu da kawo karshen fadace-fadacen da aka dade ana fama da su.

Gwamnan ya dage a kan lallai a haramta tafiya yawon kiwo, yana mai karawa da cewa ba wata hanya kan yadda za a  inganta rayuwar Fulani makiyaya muddin ba a hana su zuwa kiwo cikin tsakiya da kudancin kasar nan ba.

Tuni Gwamna Ganduje ya kafa kwamitin da zai ba gwamnatinsa shawarwari a kan yadda gwamnatin za ta kafa wa Fulani makiyaya na ko’ina a cikin jiharta rugage da za su kunshi dukkan abubuwan more jin dadin rayuwa ga Fulanin da ’ya’yansu da dabbobinsu.

Wannan fili yana maraba da wannan niyya ta Gwamna Ganduje da fatar dukkan gwamnonin jihohin Arewa da ake da Fulani za su himmatu ba tare da bata lokaci ba wajen kafa wa Fulanin rugage da wadata su da kayayyakin more jin dadin rayuwa a jihohinsu. Yanzu kuma shi ya fi dacewa, don gwamnonin su sani hakki ne a kansu su yi haka.

 

Share