✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kazafi aka yi mini,  ban ce Gabon da Maryam karuwai ne ba  –  Tanimu Akawu

Tanimu Akawu daya ne daga cikin dattawa a masana’antar fina-finan Hausa, a kwanakin nan labari ya rika yawo a kafafen sada zumunci cewa a wata…

Tanimu Akawu daya ne daga cikin dattawa a masana’antar fina-finan Hausa, a kwanakin nan labari ya rika yawo a kafafen sada zumunci cewa a wata hira da ya yi da gidan rediyon Bision FM da ke Abuja ya kira abokan sanarsa da suka hada da jaruma Hadiza Aliyu Gabon da kuma Maryam Yahaya a matsayin karuwai. A labarin an bayyana cewa jarumin ya fadi haka ne sakamakon wata tambaya da aka yi masa cewa ko mene ne dalilin da ya sa mata ’yan fim suka fi maza kudi, inda aka ce ya ce saboda suna da samari masu kudi, a karshe ma aka bayyana ya kira mata ’yan fim da suna karuwai. A hirar da Aminiya ta yi da jarumin ya ce kazafi aka yi masa, kuma yana yunkurin daukar matakin shari’a don ya nuna wa duniya cewa kazafi aka yi masa. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

A kwanakin nan an ga labarinka yana yawo a kafafen sada zumunci cewa ka kira jaruma Hadiza Gabon da Maryam Yahaya a matsayin karuwai, ko mene ne sahihancin wannan labari?

A gaskiya ba ni ba ne, na yi bakin ciki da wannan labari, a zaharin gaskiya kimanin wata bakwai da ta wuce na yi hira da gidan rediyo na Human Rights da ke Abuja, an nadi muryata, an kuma dauke ni a bidiyo, babu wurin da na kira sunan Hadiza Gabon ko Maryam Yahaya sannan na kira su da sunan karuwai.

Kimanin watanni bakwai din an yi ta kira na ana tambayata ta yaya zan yi haka? Na ce ba ni ne ba, ban fadi abu makamancin haka ba, an iya tunawa ko a lokacin ma Hadiza Gabon ta kira abokin aikina Al’Amin Buhari kasancewar ba ta da lambata, ni ma ba ni da tata, Al’Amin ya sanar da ita ba abin da na fada ba ke nan. Na samu labarin ma ta yi ikrarin kai ni kara, amma ta je gidan rediyon Human Rights din ta gane ba abin da na fada ba ke nan.

Don haka a yanzu da na ga labarin sai al’amarin ya sake daure mini kai, kodayake a yanzu na gane wata kafar sada zumunci mai suna Sarauniya ce ta yada labarin, ta hada hotona da na Gabon da kuma na Maryam Yahaya, wannan ba wani abu ba ne face sharri da aka yi mini, wata makida aka hada don a ci mutuncina, a bata mini suna, kuma ban yafe ba.

Shin wane abu ka fada a hirar da aka yi da kai kimanin watanni bakwai da suka wuce, inda har ta kai ga a yanzu an sauya mata ma’ana?

An tambaye ni ko me ya sa mata ’yan fim suka fi maza kudi da famtamawa, sai na ce dole su fi mu, domin suna yin kwalliya, kuma suna da samari masu kudi da za su ba su kudi, mu kuma maza ba a ba mu. Amma ban ambaci sunan kowa ba. An tambaye ni ko ta yaya suke samun kudi, na ce wa mai tambayar ya je ya tambaye su.

Shin ko wane abu ya taba hada ka da Gabon ko Maryam Yahaya ne da har ta kai aka ce ka kira su da sunan karuwai?

Babu wani abu da ya taba hada ni da Maryam Yahaya ko Gabon. Ban taba ganin Maryam ba duk da na shekara 20 a harkar fim, Gabon kuwa zumunci ne a tsakaninmu, ta taba yi mini hanya na samu kudi lokacin da na yi tallar kamfanin taliya na Indomie, to me ya sa zan yi mata haka?  Ina so mutane su sani cewa duk wanda yake aikata laifi sai kake yada laifinsa, to Allah Zai jarrabe ka da shi.

Ko a yanzu su Gabon sun tuntube ka dangane da wannan batu?

A gaskiya dukkansu babu wacce ta kira ni a cikinsu, ni ma kuma ban kira kowa a cikinsu ba, saboda ban fadi abin da aka ce na fada ba, in na kira su ma za a ga kamar ina da laifi.

Ko ka samu kira daga ’yan fim da kuma masoyanka dangane da wannan batu?

Eh na samu kira sama da 300, inda mutane suke kirana suke tambayar me ya sa zan yi haka, nakan sanar da su kage aka yi mini, idan kuma ba kage ba ne to a fito da murya ko bidiyon da na fadi abin da aka yi mini sharri cewa  na fada.

Ina so mutane su sani na shekara 20 a cikin harkar fim, ba na tsoron kowa, kuma ni ba mai son tashin hankali ba ne, na yi hira da gidan rediyon Faransa ma kwanaki baya kan ’yan fim da Buhari, amma ban fadi mummunan abu a kansu ba, domin ni mutum ne mai son zaman lafiya, kuma ba a taba jin abokin rikicina ba.

Don haka idan na fada ba zan yi musu ban fada ba, saboda ba na jin tsoron kowa, idan kuma da na fada sannan na gane cewa na yi kuskure, to zan fito duniya in fada in ce na yi kuskure a yafe mini, saboda dan Adam ajizi ne, amma ban fadi haka ba, wannan al’amari ya sa ni bakin ciki sosai.

Ko a lokacin da al’amarin ya faru, shin ka yi yunkurin daukar wani mataki?

Eh, na yi yunkuri don in gano wadanda suka aikata hakan amma na kasa, domin labari ne yake yawo a kafar sada zumunci kawai, ko a lokacin da aka sace mini mota na nemi a yi ‘tracking’ dinta amma abin ya faskara, shi ya sa na hakura a wannan lokaci, na ja Allah Ya isa, na kuma bar wa Allah komai.

A yanzu wane mataki kake so ka dauka?

A yanzu zan je gidan rediyo na Human Rights in sake hira. Sa’annan zan yi bincike, idan har na gano wanda ya aikata mini haka to zan dauki matakin shari’a. Ga wadanda su aikata mini haka kuwa, Allah Ya isa ban yafe ba, sai Allah Ya saka mini, sai an yi mana shari’a a ranar Alkiyama.

Mene ne kiranka ga masoyanka?

Ina so su fahimci sharri aka yi mini, na san sun ji babu dadi, amma su yi hakuri, zan bi dukkan matakan da suka kamata wajen gano wadanda suka yi mini haka. Ga ’yan fim kuwa ina so su sani ba zan taba aibata masana’antata ba, ko da ma akwai masu laifi ba zan shiga kafar yada labarai in yayata ba, sai dai in same su in yi musu nasiha.