✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ki haifi ’ya’ya 4 ki daina biyan haraji – Kasar Hungary

Kasar Hungary ta yi alkawarin yafe biyan kudin haraji ga matan da suka amince su haifi ’ya’ya har zuwa karshen rayuwarsu. Gwamnatin kasar ta dauki…

Kasar Hungary ta yi alkawarin yafe biyan kudin haraji ga matan da suka amince su haifi ’ya’ya har zuwa karshen rayuwarsu. Gwamnatin kasar ta dauki wannan matakin ne don samar da karin jama’a a kasar bayan da adadin mutane kasar ya yi kasa.

Firaii Ministan kasar Biktor Orban ne ya sanar da haka, inda ya ce, an dauki wannan matakin ne da nufin kara tallafin kudi da rangwamen da ake bai wa iyalai masu yawan ’ya’ya, don taimaka wa rayuwar mutanen kasar Hungary.

A cewar rahoton Tarayyar Turai akalla mace ta haifi ’ya’ya 5 yayin da a kasar Hungary kuwa mace ta haifi ’ya’ya 4.

A cewa Biktor, an ware kudin kasar Forints miliyan 10 (kimanin Naira biliyan 1 da miliyan 271 da dubu 861) da za a ba mata ’yan kasa da shekara 40 wadanda suka yi aurensu na farko.

Sannan an ware Forints miliyan 2.5 don sayen motoci masu kujeru 7 ga iyalan da suke da ’ya’ya sama da uku.

An dai zabi Firayi Ministan ne a karo na uku a watan Afrilun bara, inda ake fatar zai kawo tsarin da zaisa kasar ta kara yawan jama’arta, ba tare da dogaro da baki masu shigowa kasar ba.

Biktor ya dada nanata wa mutanen kasar cewa, ba ya goyon bayan shigowar baki kasarsa musamman na kasashen Larabawa, kuma kasar za ta fito da shirin ba sani-ba-sabo ga wadanda suka karya dokar kasar. Ya ce adadin jama’ar Hungary ya yi kasa da dubu 32 a cikin shekara daya.

Firayi Ministan ya kara da cewa, duk kasar da ta dogara da baki da ’yan share-wuri-zauna za ta kasance kasa mai kirkirar hade-haden jama’a.

Biktor ya kalubalanci Tarayyar Turai a kan bukatarta ta cika nahiyar kasashen da baki.

Bayan sanarwar wadanda suke sukan shirin Firayi Ministan da magoya bayan jam’iyyar adawnar kasar sun gudanar da gangami tare da rufe hanyoyin gari suna sukar shirin.