✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kifar da Gwamnatin Mursi: kasar Masar ta fada cikin rudani

A juyin mulkin da sojojin Masar suka yi kasar ta fada cikin rudani, inda magoya bayan Mursi da aka kifar da gwamna suka ki amincewa…

A juyin mulkin da sojojin Masar suka yi kasar ta fada cikin rudani, inda magoya bayan Mursi da aka kifar da gwamna suka ki amincewa da matakin da rundunar sojan kasar suka dauka, a yayin da kuma bangaren ’yan adawa ke murna da matakin.
Wannan sauyi gwamnati da aka samu, masu bibiyar al’amura sun yi hasashen kasar na iya aukawa cikin yakin basasa.
Shugaban sojojin Masar ya kawar da kundin tsarin mulkin kasar, bayan ya kawar da zababbiyar Gwamnatin Shugaba Muhammad Mursi, inda ya kafa gwamnatin wucin gadi. Wannan mataki da rundunar sojan kasar Masar ta dauka kan zababbiyar gwamnati ya haifar da rudani.
A jawabin da ya yi ta gidan talabijin, inda shugabannin soja da na addini da jiga-jigan siyasa suka tsaya a bayansa, Janar Abdel Fattah al-Sisi ya kaddamar da kawar da gwamantin Musulunci ta Shugaba Muhammad Mursi.
Jam’iyyar Mursi ta FJP, wadda Shugaba Mursi ya fito cikinta, wadda ita kanta wani rershe ne na Jamiyyar ’Yan uwa Musulmi, sun ki amincewa su gana da Sisi, inda suka jajirce kan cewa suna nan akan bakansu, shugaban da suka amince da shi shi ne Muhammad Mursi.
Gidan Talabijin na Jam’iyyar ’Yan uwa Musulmi, sun nuna zanga-zangar magoya bayan Mursi, inda dimbin al’umma suka taru a wajen birnin Alkahira.
Wakilin Gidan Talabijin na Al-Arabiya ya ruwaito cewa a kalla an kashe mutum 37, kuma wasu mutum 1600 sun jikkata.
Masu ra’ayin Musulunci sun zargi Hukumomin Masar da bude wuta a kan magoya byan Mursi a loakcin da suke gudanar da zanga-zangarsu. An kuma yi wata gagarumar zanga-zanga a gaban jami’ar Alkahira. Ministan Cikin gida ya ce za a gudanar da bincike kan wannan zargin.
Sisi ya bayar da umarnin a gudanar da zaben shugaban kasa da na majalisa, sannan ya akfa hukumar da za ta sake nazarin kundin tsarin mulki, tare da kafa kwamitin yin sasanci a tsakanin al’ummar kasar, wadanda suka hada da kungiyoyin matasa. Ya bayyana cewa wannan sabon tsarin nasa ya samu amincewar kungiyoyin siyasa da dama.
Jaridar New York Post, ta yi taken labarin lakabin “Juyin mulkin soja ya kifar da Gwamnatin Shugaba Mursi.” Kuma a wata majiyar, an bayyana cewa tun bayyan sallar magariba, Shugaban sojan kasar Al-Sisi ya bayyana wa Mursi cewa daga yanzu ba kai ne shugaban kasa ba. Shi kuwa Mursi ya ki amincewa. Wannan takaddama tsakanin masu ra’ayin Musulunci da sojojin Masar da kungiyoyin adawar siyasa na ci gaba ruruta wutar zanga-zanga, wadda ba san karshenta ba.

…‘Za mu kare halaccin gwamnatin Morsi da jininmu’

Daga Salihu I. Makera

Gamayyyar Jam’iyyun Tabbatar da Halataccen Mulki a shekaranjiya Laraba ta bukaci daidakun jama’a da cibiyoyin kasar su yi biyayyya ga tsarin mulkin kasar tare da girmama ttsarin dimokuradiyya da ya kawo Shugaba Mohammed Morsi gadon mulki.
Gamayyar wadda ta kunshi jam’iyyun Freedom and Justice Party da Ikhwanul Muslimina da Al-Watan da Al-Wasat da kuma Al-Jamaa Al-Islamiya, sun kira wani taron manema labarai a matsugunin Morsi da ke Rabaa Al-Adaweya domin nuna goyon bayansu ga Shugaban awoyi kadan kafin sojoji su bayyana kwace mulkin kasar.
Gamayyar sun nemi sojoji su tsaya kan alkawarinsu na kasancewa ’yan ba-ruwanmu a harkokin siyasar kasar, inda suka ce, “Mun ji sojoji za su kare wadanda suke Dandalin Tahrir, amma yaya za a yi da jama’ar da ken an, inji Shugaban Majalisar Dokokin kasar a taron manema labaran, inda ya yi tambayar, “Ko mu ba mu da katin zaman ’yan kasa ne? Ko mu ba mutanen Masar ba ne?”