✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Killace Fulani makiyaya wuri daya ba zai yi tasiri ba – Abubakar Sardauna

Shugaban kungiyar Miyatti Allah ta kasa, reshen Abuja da kewaye, Alhaji Abubakar Sardauna, ya ce bai dace a ce za a fito masu da tsarin…

Shugaban kungiyar Miyatti Allah ta kasa, reshen Abuja da kewaye, Alhaji Abubakar Sardauna, ya ce bai dace a ce za a fito masu da tsarin zama wuri daya ba, domin dai yanayin yawon kiwo daga nan zuwa can shi ne al’adar rayuwarsu.
Kamar yadda ya ce, wannan shiri da wasu ke ba da shawarar gwamnati ta dauka ba zai yi tasiri ba, domin kuwa abin da aka ce an gada kaka da kakanni wuyar bari gare shi. “Gado yana da wuyar bari, domin mukan zagaya daga nan zuwa can domin samun wurin da ya dace da dabbobinmu. Ba kamar dabbobin kasashen Turai ba da suka saba da a ajiye su wuri daya a kawo musu abinci, mu yanayin dabbobinmu ya zama dole a kewaya da su kiwo, sannan su samu yanayi da abincin da ya dace da su. Kuma wannan yawon kiwon ya zama rayuwa da al’adarmu.” Inji shi.
Maimakon a killace Fulani makiyaya a wuri daya, shugaban ya ce za a iya yin tsari, ta yadda idan mutum zai fita kiwo daga wata jiha zuwa wata, to ya sanar da shugaban Miyatti Allah na jihar da zai sauka, domin a san da zuwansa. Ya ce kamata ya yi a yi kwamitin da zai rika kula da wannan yanayi. Wannan kwamiti ne zai hadu da hukuma, yadda tsarin zai tafi daidai yadda ake so.
Da ya koma batun satar dabbobi nan da can da ke faruwa a sassan kasar nan kuwa, shugaban ya ce jahilci ke kawo wannan da kuma zaman banza da son rayuwa mai tsada da rashin tarbiyya daga yaransu na Fulani.
Da yake ba da shawarar matakin da ya kamata a dauka domin magance wannan matsala ta satar dabbobi, Sardauna ya ce: “Ya kamata Gwamnmati ta sanya hannu sosai wajen ilimin makiyaya. A samu agaji daga gwamnati, yadda za a koya wa yaran Fulani sana’o’in hannu da sama masu jarin tafiyar da sana’a ko aikin da aka koya masu.
“Lallai ne a kafa kungiyar sintiri ta Fulani a kowace jiha da karamar hukumna, domin babu wanda ya san sirrin Fulani sai Fulani, su suka san daji suka san sirrin dabbobi, duk satar da ake ta shanu, ba za ta yiwu ba sai da hannun Fulani.” Inji shi.
Game da shirin da kungiyarsu ke yi kuwa, ya ce: “Muna da tsare-tsare da muke yi domin ganin mun kawo karshen sace-dacen nmutane da maganar fada tsakanin makiyaya da manoma. Muna hada kai da sarakuna da shugabannin Fulani, za mu kafa kungiyar banga mai karfi ta tsaro, mu nemi tallafin jami’an tsaro, ta yadda za a rika shawo kan duk wata matsala ta tsaro. Lallai ne gwamnati ta taimaka wajen samar da burtaloli da wuraren kiwon dabbobi.”