✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kimanta kuncin kaskantar kasa

Manuniyar munin yanayi A kasashen duniya aka yi Haurobiya kan babban layi An dai samu tsautsayi Mahukunta me kuke tsimayi   Al’umma na jin jiki…

Manuniyar munin yanayi

A kasashen duniya aka yi

Haurobiya kan babban layi

An dai samu tsautsayi

Mahukunta me kuke tsimayi

 

Al’umma na jin jiki

Wadansu na ta biki

Adon-gari an rambada jam baki

’Yan lalle ana ta sakin baki

Tsofaffi na cike da mamaki

 

Kimanta kuncin kaskantar kasa

Kundumbalar  ’yan wasa

Karajin masu sa-in-sa

Karfin kwanjin kwankwasa kwarkwasa

Karfa-karfar kasurar kusa

 

Kudin cizo kwarkwata da kuma

Kamuya-muyar karma-karma

Kyankamin kyama

Kunzugun kazama

Kauyuka da birane ana hamma

 

Haurobiyawan fama

Hakilon dama-dama

Hankoron hadama

Hayagagar masu takama

Harbin karsana da guzuma

 

Macizai da kunami

Cizo da harbin karin kaimi

Miyagu masu fashi da mukami

Gyambo ne ake ta fami

Farmakin magabta da makami

 

An fitar da jaddawali

Alkaluma ne a fili

Yawan marasa muhalli

Adadin marasa hankali

Da dukiya ake fatali

 

Wayyo Direban alli

Dalibai an shirya musu kwali

Makaranta na kyalkyali

Koyi-ka-koyar ba fasali

Shagabanni na fi’ili

 

Yamadidi yai yawa

Yarfen yekuwa

Yankar yakuwa

Yanayin yadon yadiyar yadawa

Yafucen ’yan yawa

 

Giringidimin gigiwar giwaye

Gogoriyon gauraye-gauraye

Gayun gundumar gwanaye

Gumurzun gwauraye

Garnakakin gaye-gaye

 

Tukin tuwo

Damun dawo

Naman dabbar kiwo

Tiyar hatsin awo

Akushi kowa ya kawo

 

Masana fannonin ilimi

Ai watsattswake da wasali

Ku sa ai aiki da hankali

Dukiya ta zam tattali

Zalunci ya daina tsunkuli

 

A haska fitila

Kowa ya sakata ya wala

Al’umma ta ji ba wahala

A samu karsashin kawar da kasala

Zukata su faranta ba hassala

Mu daina ci wa juna kwala

Kowa ya fice daga matsala

A tarwatsa masu laluben galala

Don su dinka galleliyar galila

Wai sun samu salala

A daina yi musu talala

Su daina samun walwala

A tsula musu bulala

Sui ta lalala

Sai arzikin kasa ya malala

Kasarmu ta kayatar

Ba wanda zai kaskantar

Kyawunta yai nono tar-tar

Mun bar sha wa juna mur

Miyagun ta’adu mun ce tir

A kawar da juhala

Ai fafutikar tabbatar da adala

Faskekiyar fahimta ce falla-falla

Da karatu dalla-dalla

Sai kowa ya kula

Kowa ya bi umarni

A kiyaye hani

Mui wa juna tuni

Kar ai sabani

A daina laifi babba da kankani

Kyakkyawar ta’ada

Bin ka’ida

A riski gwaggwabar fa’ida

Rubutun alkalami da tawada

In an gaza karatu malumma su tada

A bi doka

Ka da kowa ya koka

A kauce wa kiki-kaka

Balaguro a tattaka

Ba shakkar mugu mai fatattaka

Karshen karkarewar marisar Maris da farkon tunkarar Wata-a-farin-lilon shekara ta dubu karamin lauje da sili da manuniyar kasa, ana ta yamadidi da yarfen yadon yadiyar yadawar ’yan yawa kan yadda MANUNIYAR MUNIN MATSAYI ta dora Haurobiya a babban layi. Ta yiwu a ce lamarin dai ba wani tsautsayi ba ne, don haka sai mu ce da mahukunta me kuke tsimayi?

Jerin kasashen a cewar Jam’in jami’an Jami’ar John Hopkins, su ne Benen-zuwan-lalala wadda ta rike kambinta a tsawon shekarun 2015 da 2016 da 2017 da 2018 da farfajiyar Iraniyawa da Barazana-da-zilliya da Turakun turka-tukar tunkude kiyayya ko in ce Turakun tarairayar uwa da ’ya’ya .

Ma’aunin munin matsayin muhallin mutane na bisa kan doron zaman dirshan da kashe fatari a tsakankanin al’ummar kasa da tsulin tsawwalar tsadar rayuwa, da ARON ASIN ASUSU, tare da dauke kimar dukiyar da ake hada-hadar kasuwanci ko kaso-kaso wawanci da ita a kasa. Wannan dai duk irin tsirfarsu Jam’in Damo: Je-fi Mugun, wanda ya taba fitar da Haurobiya daga jerin jadawalin manuniyar kimar bunkasar tattalin arzikin kasa ba da dadewa da darewar Baban-burin-huriyya bisa karagar mulki. Sannan an samu kwata irin wannan tsurkun tsirface-tsirface daga uwargida mai Langar Ligidin lallaga lamunin lumana ligi-ligi.

’Yan makaranta sai mu kara bitar LANGAR LIGIDIJN LAGAD da JAMI’IN DAMO: JE-FI MUGUN, tare da miyagun ayyukan kassara kasa da aka tsuwirwirta a Hauyrobiya, musamman HALIN-BURTU: A BADDA KAMA A YI BARNA da BASUSSUKAN WUNI-WUNI irin na ’YAN UWAN DA BA SU DA WANI da dai makamantansu.

Haurobiyawa, cikin shekara ta dubu karamin lauje da kofar hanci Bakin Birtaniyawan Cece-ku-ce da jaridar Gadin-yana ta Haurobiya da sauran kafafen yada kwakwazo da watsattsaken labaran duniya, sun taba baje manuniyar alkaluman jadawalin da ya tabbatar da gwaggwabar alamar FARA’AR FUSKOKIN FURANNI  a Haurobiya. Wata manuniyar ta nuna kasar nan a mataki na babban lauje a fadin Ifrikiyya, yayin da aka ce a daukacin fadin duniya ita ce ta manuniyar kasa da sili. Koda yake dai a zamanin mulkin mulaka’u ne na jam’iyya mai danboto da sanda jirge.

’Yan jam’iyya mai danboto da sanda jirge sun ayyana cewa rahoton Jami’in jami’an jam’in jama’ar Jami’ar John Hopkins na nuni da cewa Haurobiya na kara kaskanta kasa-kasa a harkar tattali. Don haka ni ma na ce su kuwa a zamanin mulkin mulaka’unsu Haurobiya ta yi matukar kasura a FANTAMAWAR FACAKAR FATALIN FATATTAKA FAMA-FAMAI da DAFDALAR DAULAR DANNE DALOLI. Kuma DANNIYA DA MURDIYYAR da ta fi fice ita ce ta MACE-DA-ZANE DA SAMUN-BOM-DA-SAUKI.

A wajen bikin yaye daliban jam’in jama’ar jami’ar Jihar Lallaga-sisi a baban birnin su Lasisi, mataimakin Baban-burin-huriyya, Usainin-Babajo ya nuna wa al’umma yadda ake tarairayar masu koyon watsattsake da fallen shafukan wagagen littattafai, inda ake dundume musu kururu da nagge da karsana dubu dari baban lauje da tsuntsayen miya dubu sili da kofar hanci da madambaci da ’ya’yan kaji wadanda ba a kyankyashe ba, har malala manuniya sama da dubu dari madambaci.

Hakika wannan martani ne ga Jami’in Jami’an jam’in jama’ar Jami’ar John Hopkins da hamshakan ’yan jam’iyya mai danboto da sanda jirge da ke murmushin murnar rahoton manuniyar mummunan matsayi ga kasar Haurobiya.

Ita dai wannan rayuwa kusan kowa ya san akwai bagiren da wani ke kwararar da kwallar hawaye, yayin da wadansu ke furkaniyar farin cikin ruguntsimin biki.

Hakika alkaluman jimamin jadawalin jinjina jajjagen jaga-jagar jigata jelen jalli-jogar jama’a a Haurobiya ta yiwu shaci-fadi ne ko zuki-ta-malle kama-kolo ka hada shi da zomo. Domin idan ba haka ba me ya sanya sai lokacin da su Baba-ojo da Gudun-loko suka jigata al’umma aka ce manuniyar farin farin-cikin fara’ar fuskokin furanninmu ta kasura?