✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kin jinin kafa ruga a Kudu na nuna zaman doya da manja suke yi da Arewa – Lawal Maidoki

Malam Muhammad Lawal Maidoki, Sadaukin Sakkwato shi ne Shugaban Hukumar Zakka da Wakafi ta Jihar Sakkwato a tataunawarsa da Aminiya kan lamarin ruga ya ce…

Malam Muhammad Lawal Maidoki, Sadaukin Sakkwato shi ne Shugaban Hukumar Zakka da Wakafi ta Jihar Sakkwato a tataunawarsa da Aminiya kan lamarin ruga ya ce kin jinin shirin kafa rugage da mutanen Kudu ke yi na nuna yadda suke zaman doya da manja da mutanen Arewa. Kuma ya tabo batun almajirci da ayyukan hukumarsa ga ke gudanrwa:

Aminiya: Me kake ganin ya janyo rashin amincewar shugabannin Kudu a kan shirin kafa rugage da Gwamnatin Tarayya ke shirin yi?

Maidoki: Wannan abin da suka yi na kin jinin a kafa rugage a Kudancin Najeriya ya fito da zaman doya da manja da suke yi da mutanen Arewa a fili. Bai kamata su shigo da addini ciki ba a kokarinsu  na nuna kiyayarsu ga Arewa da Musulumi, har a ce Bishop din Angilika na Enugu Rabaran Emmanuel Chukwuma ya fito yana gargadi ga gwamnonin yankinsa cewa kada su ba da filin yin ruga, kuma duk wanda ya aikata haka za su yi yadda zai rasa kujerarsa ko da karfi. Ka dubi wannan magana kamar ba aikin kasa ne ba da ake sa ran warware rikici a tsakanin manoma da makiyaya. Duk tsarin da aka fito don warware wannan matsala sun ki kallonsa da idon basira suna ganin Fulani ne kawai za a taimaka. Bayan wannan shirin taimakon kasa ne da zai samar da ingantaccen nama da madara. Sun yarda a kai musu shanun  da Fulani makiyaya suke kiwatawa su saya su ci nama, amma ba su yarda a samar musu da matsugunni a wajensu ba. Akwai rainin hankali a nan.

Aminiya: Yaya kake kallon matsalar almajirci a kasar Hausa kana ganin ya kamata a kashe shi?

  Maidoki: Almajirci ko a wurin masu nazarin harshen Hausa kalma ce mai kyau kuma a kira ka  almajiri wani matsayi ne da al’umma take bai wa mutum yana nuna mutum mai neman ilimi. A Musulunci kuwa neman ilimi wajibi ne ga dukkan mutum baligi mai hankali, neman ilimi ba bakon abu ba ne, a kowace nahiya kana samun mutane suna tafiye-tafiye wajen neman ilimi.Amma a yanzu an mayar da kalmar almajirci ga yara masu yawon bara, alhali almajirci daban yawon bara daban. In wadannan yara da ke yawo a tituna su damu mutane ba almajirai kadai ne ke yawon bara ba. Da maroka da ’yan bangar siyasa da bambadawa duk mabarata ne, in za a hana, dukkansu za a hana. Ba ina goyon bayan bara ba ne, yaro dan shekara biyar ko kasa da haka ya rika yawo lungu da sako cikin dauda ya baro mahaifansa yana yawo ba daidai ba ne, kamar yadda eriya bois ke kiran kansu matasa suna abin da bai dace ba, kamar yadda yaran da ke makaratar boko ke yin abin da bai dace ba, ba a damuwa saboda Allah suke sabawa, dukkan wadannan ba daidai ba ne. Wannan bara da iyayen yara suka turo su su je su nemi abinci da kansu kuskure ne. Da can inda aka fito akwai tallafi da ’yan uwantaka a cikin al’umma in aka ga bako ko ba a san shi ba za a taimaka masa, akwai mutunci da zaman lafiya. Almajiri har gidan zama ake yi masa in an yi ruwan shuka ya koma gida, wannan ba laifi ba ne, amma tura yaro karami wanda bai san yau ba balle gobe a saka shi a titi ana iya maganinsa in hukuma ta bi hanyar da ta dace.

Aminiya: Kana ganin sanya yara a makarantar boko zai magance tururuwarsu zuwa birane, ko dokar da Shugaban Kasa zai yi za ta magance wannan?

Maidoki: Wannan abu ne mai kyau in zai iya, sai dai ina son ya gwada ko za a samu nasara. Akwai abubuwa da yawa da suka kamata a gyara kafin wannan magnar. Ina Hukumar Ilimin Yara (UBE) da ta makiyaya (NOMADIC), shirin na almajirci an fito da shi kafin zuwansa, me ake ciki? Matukar ba a yarda Allah Ya zama saman komai ba, a sanya Shi cikin aikin gwamnati a yarda da tsarinSa, babu abin da zai canja. A dokar ma tana bukatar sanin halin mutane a san me ya sa yaran ba su zuwa makaranta kauyukan da da ke da makaranta ba malamai yaya za a yi da su? In Shugaban Kasa na son samun nasara ya nemi sarakuna da malamai masu jin tsoron Allah su fada masa gaskiya a hadu a warware matsalar a hankali ba  rana daya ba.

Aminiya: A ganinka me ya sa mutane suka dauki karatun boko ne kadai ilimi mai amfani?

Maidoki: An wanke musu kwakwalwa sun mance da Allah sun wulakanta iliminsu na addinin Musulunci. Sannan wadansu sun dauki Bature a matsayin Ubangiji ba wani gabansa. A Musulunci gara ka mutu da talauci kana da imani da ka mutu da dukiya ba imani, babu abin da ke kanmu kamar fahimtar addini. Duk ilimin da za ka samu ba wannan ba ci baya ne don gardama da fitina ce kawai a gabanka. Kuma muna bukatar a dawo mana da boko cikin harshenmu duk kasashen da suka ci gaba da harshensu suke koyar da fasaha da kimiyya. Dubi Fotugal da Tailan da China da Indiya da Beljiyum da Habasha. Amma sai ka ga a jihohinmu na Arewa a tura yara su yi shekara biyu suna koyon harshen Bulgeriya kafin su fara karatun likitanci in sun mutu littafansu ba su da amfani ga ’ya’yansu, wannan kuskure ne. Mutum ya yi tunanin ba ci gaba sai an iya harshen Turawa, birbishin wankin kwakwalwar da aka yi wa wadansu tsofaffin ’yan boko ne. Ya kamata a dawo a rika koyar da yaranmu da harshen Hausa da Ibo da Yarbanci a koyar da kowane yaro da harshensa a ga abin da zai faru nan gaba kadan a fagen kimiyya da fasaha. Kada ka manta muna da ilimin jima da saka tun da can balle yanzu a ce muna cikin masu jahilci. Yaron da ke da ilimin addini a ce ba mai ilimi ne ba wanda ya yi ilimin boko shi ne mai ilimi wannan kuskure ne. Wani dan boko sai ya ji ina maganar da ba ta yiwuwa saboda kwakwalwarsa na cikin mallaka. Matukar ba mu gyara ba, za mu rasa harshenmu da al’adarmu da yawa za a rasa addini.

Aminiya: Tallafin da kuke bayarwa a wannan hukumar taku wane tasiri ya samar a rage talauci a Jihar Sakkwato

Maidoki: Wannan tambayar na da wuyar amsawa. Wannan aiki  muna yin sa ne don Allah, gwamnatin Sakkwato muke wakilta. Gwamnati da Majalisar Sarkin Musulmi suna taimaka wa hukumar nan sosai, hakan ya sanya aka samu nasarar taimakon da muke yi ga mata da matasa a harkokin sana’a da wayar da kan jama’a da masu karamin karfi. Tambayarka na so ka yi wa mutanen gari ne don ayyukkan da muke yi ba su tafiya da lissafin kididdiga. Amma in kana halartar tarurrukanmu ka ga yadda muke tallafa wa masu karamin karfi da marasa lafiya da masu tabin hankali, da za ka hada wadanda hukumar ta tallafa mawa za su kai fi dubu 100 zuwa dubu 500. Ka tambayi mutane za ka iya samun amsar da za ta gamsar da kai.

Aminiya: A ziyarce-ziyarcen da ka kai ga hukumomin zakka da wakafi na kasashen duniya ko akwai wasu ayyukka da kuka fara aiwatarwa da ka kwakwaya daga takwarorinku?

Maidoki: Hikima kayan mumini ce, akwai abubuwa da ingantattun aiki da muka dauko kamar kula da tsofaffi da ciyar da su da muka kwaikwayo a Afirka ta Kudu, ga haduwarmu da mutanen kasar Katar suna gina mana gidaje a Sakkwato goma sha wani abu suna taimakon marayu da mabukata da abinci. Akwai shirin tallafa wa ’yan gudun hijira da sauran abubuwa da dama don ciyar da al’ummarmu gaba.

Aminiya: Ko akwai wata jiha da ta nuna sha’awarta ta kwaikwayi abin da Sakkwato ke yi a fannin zakka da wakafi.

Maidoki: A gaskiya akwai jihohi da yawa da ke son yin abin da Sakkwato ke yi irin su Kogi da Adamawa da Bauchi da Legas da Borno da Yobe da Neja da Kebbi. A Jamhuriyar Nijar, Minista da Gwamna sun zo inda Sarkin Musulmi da Gwamna suke son yin alaka da hukumarmu mun zauna da su sun gayyace mu don a kara zuwa a yi wa jama’ar can bayanin ayyukan zakka da wakafi.

Aminiya: Ina aka kwana kan shirinku na samar da wakafin asibiti da dakunan kwanan dalibai a manyan makarantun Jihar Sakkwato?

Maidoki: Gwamna zai ba mu babban fili da za mu dasa itatuwa da wani da za mu yi cibiyar da za a samar da gidajen kwanan dalibai da gidan burodi da asibiti da makaranta wadanda masu ba da tallafi na Katar za su gina mana. Za mu samar da gidajen kwanan dalibai a Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere ta Umaru Ali Shinkafi. Wakafin asibiti kuma Ma’aikatar Lafiya ta Jiha tana ba mu hadin kai dari bisa dari an hannunta mana Asibitin Farfaru wanda ke kan Titin Filin Jirgin Sama, yanzu asibitin ya dawo karkashin kular Hukumar Zakka da Wakafi. Za mu yi kokari mu bunkasa shi ya zama wurin zuwan mai karamin karfi. Asibiti ne kamar kowane sai dai za a ci gaba da duba yanayin mutum da rashin lafiyarsa wajen karbar kudinsa. Ba za a yi yajin aiki a asibitin ba, za a yi sharadi da duk wanda zai yi aiki wurin don aikin Allah ne.