Categories: Wasiku

Kira ga Gwamnan Yobe kan badakalar da ake yi a Kungiyar NECAS

A yau ina so ku ba ni dama in yi kira ga Gwamnatin Jihar Yobe a karkashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni dangane da ta’asar da ake zargin ana tafka wa a kungiyar nan ta North East Commodity Association (NECAS) wadda take ba da bashin kayan noma ga manoma don tallafa musu daga Gwamnatin Tarayya.  Muna amfani da wannan dama wajen sanar da Gwamnatin Jihar Yobe cewa, ana tilasta wa jama’a sayar da kayansu ga wadansu ’yan kasuwa ba tare da kayan ya iso hannun manoman ba. Kuma idan har mutum bai yarda ya sayar da nasa kayan ba, zai yi wuya wannan kungiya ko hukuma ta ba ka kayanka a kan lokaci ko ka samu kayan gaba daya. Domin kuwa har yau akwai mutanen da ba su sayar da nasu kayan noman rani ba har yau da muke cikin damina, ba a ba su wasu daga cikin kayan noman ranin nasu ba, sai dai ana ta sanya masu lokaci. Shin Gwamnatin Tarayya ce da kanta ba ta aiko ba ko sun makale a hanya ne? Kamar yadda Gwamnatin Tarayya ta kirkiri wannan shiri don tallafa wa manoma kuma ya zamto bashi, ya kamata a yi wa al’umma adalci a rika ba su kayayyakinsu hannu-da-hannu don su ci moriyarsa. In mutum ya yi ra’ayi ya yi noma da kayansa in kuwa ya yi ra’ayi ya sayar da kayansa ga wani dan kasuwar daban, tunda dai ya san bashi aka ba shi, ba wai a rika tilasta wa jama’a su sayar wa wadansu tsirarun ’yan kasuwa ba, suna saya yadda suka ga dama. Muna kira ga Mai girma Gwamna Mala Buni idan Allah Ya sa wannan sako ya kai gare shi ya sa a yi bincike a wannan hukuma ko kungiya don gano gaskiyar al’amarin tare da daukar mataki a kai.

Daga Sa’idu Abdullahi, Damaturu Jihar Yobe, 08032127482.

ADVERTISEMENT

ADVERTISEMENT
..

Recent Posts

An rantsar da sabon Mataimakin Gwamnan Kogi

Duk an kammala shirye-shiryen rantsar da Edward Onoja a matsayin sabon Mataimakin Gwamnan jihar Kogi. Babban alkalin jihar Nasir Ajanah,…

6 hours ago

Yau Buhari zai ziyarci kasar Rasha don halartar taro

A yau Litinin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, zai ziyarci birnin Sochi a kasar Rasha don halartar taron  kwana uku wanda…

6 hours ago

Matashin da ke sace kudin coci ya shiga hannu

Wani matashi da ake zargi da sace kudin da ake tarawa na sadaka a cocin "Divine church of God" a…

7 hours ago

‘Yan Sanda sun bada belin Malam Niga a Kaduna

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kaduna ta bayar da belin Malam Lawal Yusuf Muduru da aka fisani da Malam Niga wanda…

19 hours ago

An yi garkuwa da Mataimakin Kwamishinan ‘Yan sanda

Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da yin garkuwa Kwamandan shiyyar Karamar Hukumar Suleja kuma Mataimakin Kwamishinan ‘yan sanda ACP Musa…

1 day ago

An gano zakin da ya tsere daga gidan zoo na Kano

Bayan shafe daren jiya ana neman wani rikakken zaki da ya kufce daga gidansa a gidan namun daji na Kano,…

1 day ago