✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kira ga Gwamnatin Zamfara kan janye dokar takaita zirga-zirgar babura

Don Allah ina so a ba ni dama in yi kira ga hukumomin jiharmu ta Zamfara da su dubi yiwuwar janye dokar takaita zirga-zirgar babura…

Don Allah ina so a ba ni dama in yi kira ga hukumomin jiharmu ta Zamfara da su dubi yiwuwar janye dokar takaita zirga-zirgar babura daga karfe 6 na yamma zuwa karfe 7 na safe, wanda gwamnatin ta saka a watannin baya, duba da yadda zaman lafiya sai dada samuwa yake a sassa da dama na jiharmu, sannan a yanzu wasu daga cikin jami’an tsaro musamman ’yan sanda suna amfani da wannan doka wajen karbar kudi a hannun al’umma, don haka muke kira ga hukumomin jiharmu, tunda dama an sanya wannan doka ce saboda tabarbarewar tsaro, to yanzu tsaro ya samu a jihar. Don haka su janye mana wannan dokar, domin al’umma su dawo ga harkokinsu na yau da kullum yadda aka saba. Da fatan kirana zai kai ga kunnuwan da aka yi dominsu. 

Daga Mahmud Salihu kauran Namoda, Zamfara. 09079551996