✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kira ga ’yan Najeriya kan kishin kasa

Matukar al’umma za su kasance ’yan tsaki da tunani irin na dila da dabi’ar zaki a dawa, to wannan al’umma ta kara lalacewa za ta…

Matukar al’umma za su kasance ’yan tsaki da tunani irin na dila da dabi’ar zaki a dawa, to wannan al’umma ta kara lalacewa za ta rika yi. Rayuwa irin ta dan tsako komai ya samu  shi kadai ne ba ta dace ba. A yau ba ma kishin kasarmu, mutum kawai matansa da ’ya’yansa kawai yake yi wa hidima bai damu da al’umma ba. Dabi’ar dila kuma shi ne wayo. A yau tunaninmu yaya za samu ko da wani zai rasa. Dabi’ar zaki da muka dauka ita ce danniya da nuna isa a kan na kasa. A yau kowa ya samu dama sai ka ga zaluncinsa ya bayyana a fili. Gaba daya sai ka rasa wane ne mai gaskiya a cikinmu. Idan har muna so kasarmu ta ci gaba, ta zama abar koyi dole sai mun dauki kishin kasarmu, mun sa a zukatanmu, mun kuma cire kabilanci na yanki, harshe, addini a dukan lamuranmu.

 

Daga Nasiru Kainuwa Hadeja 08100229688/09073801967