Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Kirkiro karin Masarautu a Jihar Kano Alheri Ne – Surajo Umar Wudil

Surajo Umar Wudil

Mataimaki na musamman a kan ayyuka da gidaje ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, Surajo Umar Wudil ya ce hakika kirkiro karin masarautu da aka yi a Jihar Kano wani babban alheri ne ga jihar da al’ummarta da ma kasa baki dayanta.

ya bayyana hakan ne, lokacin da yake zantawa da wakilinmu. Ya ce babu ko shakka gwamna ya yi hangen nesa wajen datsa jihar zuwa gida hudu, yace duk wani mai su kan Karin kirkiro masarautu, ba dan kishi kano bane, ya kara da cewar ai a ko ina ana bukatar samun ci gaba, kuma a tarihin Kano, a yau ne aka fara kirkiro masarautu ba, an yi a can baya,kuma an ga irin ci gaban da hakan ya kawo ga kuma saurin ci gaba a wadannan yankuna da kuma kusan tar da jama’a ga  masu mulkinsu.

ADVERTISEMENT

Haka zalika yace babu wata maganar siyasa akan wannan lamari, abin da ya can canta ne, aka yi kuma duk masu cewar akwai matsala tsakanin Gwamna da Mai martaba sarki, ba gaskiya bane.an yi hakan nan da kyakyawar manufa, ba da niyyar cin zarafin wani ba. Domin kirkiro masarautun zai kawo bunkasar yankuna, hakazalika harkar tsaro za ta bunkasa domin za a samar da karin hakimai, masu unguwanni da dagatai, Kuma mu a matsayin mu na al’ummar Wudil muna nan da goyon bayanmu ga Masarautar Gaya.

Surajo Umar ya kuma kara da cewar jama’a jihar kano, suna sane da rin tarin aiyukan alheri da shi Gwamna Ganduje ya aiwatar a shekaru hudu da suka shude, duba da irin halin da ya karbi  jihar a waccan lokaci,saboda da zuwan sa  ya ci gaba da aiyukan da ya tarar ba a kammala ba, haka ya bude aiyukan raya kasa, ba kawai ga cikin kwarya birnin kano ba, hatta dukkan kananan hukumomi 36 da basa cikin kwaryar Kano sun amfana da aiyukan da Gwamna yak e gudanarwa a fadin jihar kano.

ADVERTISEMENT

Sai ya bukaci al’ummar Jihar Kano da su ci gaba da ba wa gwamnati duk wani goyon baya da yakamata, domin a wannan karo na biyu, za a samar da kyakyanwan ci gaba. Idan ka duba za ka ga cewar a tarihin Jihar Kano gwamna ganduje ya kasance daya daga cikin ‘yan kalilin da suka yiwa Jihar Kano aiyuka da za ka shafe shekaru da dama an cin moriyarsu ya bada misali ga giggina hanyoyi a yankuna karkara masu tsawon kilomita 150. Surajo Wudil yace In banda jihar legas babu wata jiha a duk fadin kasar nan da ta samu dandanon dimokaradiyya kamar jihar kano, domin haka al’ummar jihar su ci gaba da bada hadin kansu ga Gwamna Ganduje a wannan zango na biyu, a zangon farko shirin nan na loko kalkal, karkara salamu alaikum, wannan shiri na gwamnatin jihar kano ya nuna yadda ake kula da kananan hukumomi, na samar musu da hanyoyin karkara, da rufe kwatoci da sa interlock da fitulun kan titi a kowanne lungu, domin hana yaduwar cututtuka da kuma tsabtace gari, wanda wannan shiri ya zaga ko’ina a fadin jihar domin gwamnati ta damu da rayuwar al’ummata, haka zalika ma a wannan zangon mulki na biyu babu abin da za a fasa domin bunkasar jihar.