✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kisan da mata ke wa mazansu a kasar Hausa

Tauye wa mata hakkokinsu, muzgunawa, mugunta, son kai, rainin hankali da mulkin kama-karya daga wadansu maza su ke jawo kisan mazan aure a kasar Hausa.…

Tauye wa mata hakkokinsu, muzgunawa, mugunta, son kai, rainin hankali da mulkin kama-karya daga wadansu maza su ke jawo kisan mazan aure a kasar Hausa. Daidai ne matan auren da ba su ga ire-iren laifuffukan da aka jero ba. Yawancin mata sun sha duka, wadansu sun sha fyade, wadansu sun zauna cikin ukubar auren dole. Wadansu an raba su da ’ya’yansu an sake su, ga su nan dai barkatai. Sai dai kawai tarbiyar da daukar aure ibada ya sa suka dauki hakuri.

Amma a yanzu harkar shan Benylin da Taramadol ta watsar da tarbiyyar wadansu matan. Ga halin rayuwa da ake ciki ya yi tsanani. Mafita daya ce kawai maza su fara tuna cewa mace fa mutum ce mai rai kuma ita ma Allah Ya halicce ta ce don ta bauta maSa. Ba kaya ba ce balle a mallake ta. Ba sutura ba ce, balle a saka a cire yadda ake so. Ba akuya ba ce, tana da kwakwalwar tunani, tana da zuciya kuma duk rauninta, ba a fi ta iya mugunta ba. Sai dai Allah Ya saka mata zurfin tausayi da kauna da kiyayewa.

A duk inda namiji Bahaushe dan Arewa ya samu kansa, ya san cewa lokaci ya zo da zai sake duban da yake wa matarsa ta aure in har yana neman tsari da wuka.

Kada ka dauka tamkar ’yarka ce ko uwa ko kanwa. Don an auro mace ba ta zama baiwa ba. Amma idan aka ce sai an tankwarata don dole sai an muzguna mata an walakanta ta. To fa Benylin da Taramadol za su kai mata dauki. In kuma sun zo to hankali ya gushe sai illla masha Allahu ke nan.

A daina duka da cin zarafi da cin zali kuma a daina muzanta mata. A rika daukar nauyinsu daidai gwargwado kuma a tallafa musu su nemi na tsira da mutunci.

Duk mace mai kamar mace wadda ta amsa sunanta ’ya mace, a cikin hankalinta, ba za ta kashe mijinta ba. Wallahi in ka ji kida, da labari. Sanin da na yi wa wadansu mazan ko Shaidan bai kai su hassada da mugunta da cin zali ba. Abin haushin haka muke zaune a cikin unguwanninmu sakaka. Ba ruwan kowa da kowa, limamin da zai daura aure ba ruwansa da ko auren ya dore ko ya mutu. Saki uku ba labari ba ne mai dumi labarin shi ne yaushe za a kara aure? Burin yawancin mazanmu ke nan, sun kai matsayin kara auren ko ba su kai ba? Oho.

Aure kawai za a kara, a saka mata cikin kuncin talauci. Wadansu mazan kuma ko kaji hudu ba za su iya kiwatawa ba amma sai sun tara mata hudu. Ga yawan zance da mata a waya mai amfani da yanar gizo. Ga karya kamar ragowar yayi. Sannan babu kokarin biyan bukatun matan da ake tarawa. Me zai hana a samu matsaloli?

Gaskiya ya kamata hukuma ta tashi tsaye ta kwato wa mata hakkokinsu domin barinsu su kadai, su kwato wa kansu hakki shi ke jawo a yi mutuwar kasko. Wa gari ya waya? Dukkan al’ummar Musulmi.

Su ma matan na da laifuffukansu amma kifi daga ka yake rubewa. Idan aka samu namiji mai adalci da hankali, shi ke jan ragamar gidansa. Malamanmu na addini suna iyakacin kokarinsu wajen fadakarwa kan aure. Zaman aure da biyayya ga miji, sai dai kullum zancen gizo bai wuce na koki. Mata su yi bautar aure don Aljannarsu na karkashin kafar mijinsu. Shin ina Aljannar maza take? Karkashin kafar wata macen uwarsa. Wannan ya nuna da mace da namiji akwai bukatar adalci kuma Allah Ya tabbatar da hakan. Ya kamata malamanmu su mai da hankali wajen shawo kan izgili, wulakanci, rikon sakainar kashi da kuma watsi da maza ke yi ga rikon aure. Auri-saki, saki sakaka, dukan mace, barinta cikin yunwa da nau’o’in wahala, sun yi kanta a wajen mazan Arewa. Watakila rashin yawaita wa’azi a kansu yake sa su rika tunanin mace ba ta da hakki wajen mijinta. Su ne ’yan gatan Musulunci. Don su aka yi duniya aka halicci mace don jin dadinsu. Jahilci dai tsagwaronsa.

Iyaye  ma na da laifi wajen tursasa ma’aurata su zauna tare a lokacin da aka samu matsala. duk da cewa hakan na da wuyar gaske. A rika barin ma’aurata su rabu ko da na lokaci kalilan don a fahimci matsalar da ke damunsu. Auren dole da zabar wa mace mijin da ake ganin ya fi wa iyayen maimakon wanda take so yake son ta. Tsabar tsaurin  ra’ayi da karfa-karfa irin na uba Bahaushe yakan kawo matsala sosai, iyaye mu rika hangen nesa.

Hukuma kuwa tuntuni ta saki bakin zaren. Duk kotun da ka je ana shari’ar aure za ka tarar macen ce a kasa. Sai dai idan ’yar wane ce to nan da nan za ka ga an ba ta takardarta. Ana tauye wa mata hakkinsu bila adadin kuma jama’a da yawa ba su sani ba, ba su damu ba.

A wani mako na taimaka Hisbah suka yi sulhu a kan wani aure inda mata uku suke dukan ta hudun. Sun maida ita jaka shi ko oga, bai da ta cewa, Sun fi karfinsa. Saboda Allah idan wannan ta caka masa wuka wata rana a yi mamaki?

Kwanan nan na yi wani sulhu mai ban haushi wanda daga karshe dai an rabun. Miji ne ya kara aure.ya tattara nasa- ina-nasa ya bar gidan uwargida ya tare ana amarya. Ba ya ko leka wancan gida. Daga karshe, bayan shekara biyu ya ce ya saki uwargidan da yara biyu. To su ma ’ya’yan an sake su ke nan? Domin ya daina ci da su? Ita ma wannan idan ta caka wuka lokacin ne za mu fara surutai. Kafin sannan fa? Ina za ta je?

Jama’a duk da zamani da tabarbarewar al’adu da rashin biyayya ga addini da miyagun kwayoyi da ake fama da su. Mu ma da halayenmu na rashin tausaya wa mata. Danne hakkinsu, wajen hana su neman na rufin asiri. A hana mace aiki, ko sana’a. A bar ta cikin jahilci, a bar ta da talauci sannan a rika fantamawa ana sheke aya. Ka ga namiji na saka sutura, ya hau mota mai tsada, ya karade gari yana bagu, amma bai bar kwabo a gidansa ba. Idan ka tambaye shi sai kumfar baki yana cewa to me ta rasa? Tana ci tana sha, sai kace rayuwa don ci da sha aka yi ta. Malam Bahaushe da ban haushi yake.

Abin takaici ga tonon asirin matansu kamar ba ibada ake yi ba. Wani idan ya rika tallata matarsa, sai ka zaci wata babbar makiyiyarsa ce. Har rigima zai rika jawo wa matarsa, da surutu da gulma da sharri duk a sunan aure. Amma fa shi ya wuce mace ta koka a kansa. Idan ta bude baki ta shiga uku. In ta bari aurenta ya mutu, za ta sha wulakanci a gidansu, unguwarsu da cikin kawayenta. Idan ta zauna ta dawwama cikin bacin rai. Gaba kura baya sayaki ke nan.

Idan kuma mai hali ce aurenta ya mutu sai ka ji ana ai wance ta kashe aurenta. Kai ka ce igiyar saki uku na hannun mace.To yau ga shi kisan miji ya zaman ruwan dare, ga kisan kai da kai. Ga shan kwaya, duk a suna aure.

Maganin matsalar kisan miji shi ne a kwato hakkin mata.

  1. A ba su ilimi mai zurfi na boko da addini. Ko daga wane zango ne, a koma makaranta.
  2. A bar su su auri wanda suke so. A yi musu nasiha a tsaya nan.
  3. A bar matar aure ta kama sana’a. Kada a tilasta mata karbar ’yan canjin da ke hannun miji. Ko raba kwabo da kishiyoyi wanda hakan ke jawo rashin zaman lafiya.
  4. Kafin a yi kishiya, a tabbatar an samu yardar uwargida. A sanar da iyaye su yi mata nasiha. A hada ta da liman ya yi mata wa’azi. A ba ta hakuri sannan ita ma amarya a ja kunnenta.
  5. Dole hukuma ta fara tantance irin zaman auren da ake yi. A fadada aikin Hisbah. A shigar da mata ciki sosai. A ba wa hukumar karfin gaske na daure masu laifi da yanke hukunci mai karfi. Duk wanda ya wulakanta aure, a yi masa hukunci. Har matan ma a hukunta masu laifi. A ceci wadanda suka dulmiya cikin shan kwaya, a taimaki wanda talauci ke kawo wa rayuwar aurensu barazana.

6  A fara daure iyayen da suke auren jari ga ’ya’yansu, wadannda suke sai da ’ya’yansu don neman duniya. Sannan a rage auren wuri, a bar mata su mallaki hankalinsu daidai gwargwado.

  1. A duba katsalandan da surukai suke yi a cikin aure. Musamman matsalar uwar miji da kannen miji mata da mugayen abokai. Yawancin aure su suke kashe shi a zamanin nan namu.
  2. A rika ilimantar da ma’aurata. Duk namijin da macen da za su yi aure sai sun yi bita kamar alhazai, sai an tabbatar sun san hukunce hukuncen aure.
  3. A kafa hukumomi kamar haka:

_ ofishin bita kan aure.

_ ofishin agaza wa mata masu matsalar aure da ta danganci auren dole, duka, fitinar suruka, da sauransu.

_ ofishin kare mata daga rashin muhalli, sutura ko abinci wanda zai bai wa mata mafaka idan an koro su daga gidan miji kuma uba ya ce kada ki doshi inda yake.

_ ofishin koya wa mata zaman aure. Gyaran jiki, girki, da lura da yara, daukar ciki da haihuwa da sauransu.

_ ofishin samar da sana’o’i. Da karfafa makarantun yaki da jahilci.

Duk wadannan gwamnati na iya saka kungiyoyi masu zaman kansu su dauki ragamar aikin da taimakon gwamnati da masu halin taimakawa.

Mu ceci al’ummarmu domin aure shi ne ginshikin al’umma. Idan ya lalace, ya zama tamkar  filin yaki, to jama’a za su rasa tarbiyya da makoma mai amfani.

Watakila ma wannan shi ne tushen matsalolin da suka addabi Arewacin Najeriya. Yawaitar talauci, rashin ilimi da cututtuka wadanda suka danganci kazanta da rashin abinci mai gina jiki.

Allah Ya sa mu fahimta kuma Ya yi mana  jagora, inda muka yi kuskure Allah Ya yi mana gafara. Amin summa Amin.

 

Binta Sule Gaya  (08023099929)