✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kisan dan jarida mai kare hakkin masu auren jinsi ya tada kura a Kamaru

Gwamnatin Kamaru tare da wasu kungiyoyi masu kare hakkokin masu auren jinsi (‘yan luwadi da madigo) na yin musayar sakonni masu karo da juna a…

Gwamnatin Kamaru tare da wasu kungiyoyi masu kare hakkokin masu auren jinsi (‘yan luwadi da madigo) na yin musayar sakonni masu karo da juna a tsakaninsu. Hakan ya biyo bayan kisan da aka yi wa Eric Lembembe wani dan jarida mai fafutukar hakkin masu auren jinsi. Wasu lauyoyi da suka hada da Alice Kom sun koka kan rashin daukar wannan batu da muhimmanci da ’yan sandan gudanar da bincike ba su yi ba, ganin cewa ba su bi diddigin labarin ba, ballantana ma, a take, su gano wadanda suka yi kisan. Ita kuma Gwamnati, a cewar Ministan Sadarwa, Issa Tchiroma Bakary, an riga an gudanar da bincike a kan gawar Eric Lembembe, domin gano musababbin mutuwarsa. Kuma an umarci kamfanonin sadarwa, su fitar da sunayen wadanda ya zanta da su gabannin mutuwarsa. Majalisar dinkin Duniya ta fara matsin lamba kan lallai a kafa kwamitin bincike, don gano musababbin mutuwar Eric Lembembe.
Issa Tchiroma ya ce, gwamnati ba ta nuna wariya ga masu akidar ’yan luwadi. Saboda haka ba ta zauna ba, tana daukar matakan da suka dace, domin ganin an gano musabbabin kisan Eric Lembembe din.
Sai dai kuma kamar akwai alamun cewa wannan batun na Minista bai gamsar da wasu kungiyoyin kare hakkokin dan Adam ba, saboda tuni suka sa hannu a kan wata takardar korafi, inda suka nemi Shugaban kasa Paul Biya ya yi ganawar gaggautawa, inda aka tattauna kan daukar mataki da zai kawar da kyamar da ake yi ma wasu jama’a.
kungiyar wasu lauyoyi da ake kira Abocats Sans Frontieres. Doka a Kamaru dai ta haramta aikata luwadi, ballantana ma auren jinsi daya, dokar da ta bakanta wa Kamaru fuska ke nan a gaban wasu kasashen yammacin duniya wadanda suke riya cewa, Gwamnati na take hakkokin jama’a.
 Duk da wannan matsayi na Kamaru, Ministan Sadarwa ya bayyana a ranar Talatar nan a wata kotu ta zartar da hukunci a kan wasu mata biyu, wadanda suka aikata laifin madigo da kowacensu ke da shekaru 27 a duniya.  An yake musu hukuncin zaman gidan yari na tsawon watanni tara.
Wannan al’amari ya faru ne a watan Janairun bana, bayan Clarisse ta kai karar Jeannine a barikin jami’an tsaro na Jandarma kan cewa ta yi mata barazanar kisa, bayan wani sabanin da suka samu sakamakon madigon da suka yi.