✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kisan dan kwallo ta tada kura a Jihar Ogun

A ranar Asabar da ta gabata ce wasu ’yan sandan da ke sashin yaki da manyan laifuffuka da ake kira ZIS SARS suka kama dan kwallon…

A ranar Asabar da ta gabata ce wasu ’yan sandan da ke sashin yaki da manyan laifuffuka da ake kira ZIS SARS suka kama dan kwallon kulob din Remo  Stars, da ke garin Shagamu mai suna Tiyamiyu Kazeem,  lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarsa ya kuma so tada kura a garin Shagamu da Jihar Ogun baki daya.

A ranar da lamarin ya auku Rundunar ’Yan sandan Jihar Ogun ta bakin Kakakinta DSP Abimbola Oyeyemi, ta ce wani jami’inta ne ya kama marigayin wanda ake zargi da sanya kayan sojoji yana cin zarafin jama’a, sai dai bayan da dan sanda ya kama shi yana kan hanyarsa ta kai shi ofishin rundunar a Abeokuta daga garin Shagamu sai motarsa ta lalace yayin da dan sanda ya sauka zai gyara motar sai dan kwallon ya balle kofa yana kokarin tserewa sai wata mota ta buge shi lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarsa. Ya ce Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kenneth Ebrimson ya bada umarnin yin bincike domin ladabtar da dan sandan bisa sakaci da barin wanda ake zargin ya tsere lamarin da ya yi sanadiyar rasuwarsa.

Sai dai abokin marigayin dan kwallon mai suna Sani Abubakar, wanda yana tare da shi lokacin da ’yan sandan suka kama shi, ya musanta bayanan da Rundunar ’Yan sandan Jihar Ogun din  ta bayar dangane da mutuwar abokinsa, inda ya ce su biyu jami’an rundunar suka kama sannan su ne suka hankado abokinsa daga cikin motarsu inda ya fado wata mota da ke tafiya a bayansu ta take shi. Ya ce ’yan sandan sun kama su ne a lokacin da marigayin ya ajiye motarsa a gefen hanya zai sayi bakin mai a lokacin da suke  hanyarsu ta zuwa gaida mahaifin marigayin. Ya ce ’yan sandan sun zo a lokacin da marigayin ya je ya sayo bakin man.

“Da suka zo sun tambaye ni wa ke da motar?  Na ce ta abokina ce, sai suka karbi wayar salulata da tasa da ke hannuna. Da marigayin ya zo sai suka kama shi, suka ce mu masu damfara a Intanet ne Yahoo Boys. Sai marigayin ya nuna musu katin shaidarsa na kwallon kafa, amma suka kawar da kai suka sanya mu a motarsu suka ce za su kai mu ofishinsu a Shagamu. Da muka ga sun sauya hanya sai na fara magana ina za su da mu? Sai suka ce za su harbe ni. Daga nan ban kuma magana ba ana haka ne suka hankado abokina inda ya fado wata mota ta buge shi,” inji shi.

Ya ce “Nan da nan muka yi kokarin kai shi asibiti a motarsa domin ’yan sandan sun ki yarda mu saka shi a motarsu. Ko da muka je asibitin ya riga ya rasu, su kuma suka tsere. Da farko har na rike wani a cikinsu ina kururuwar ni ma su kashe ni yadda suka kashe abokina.”

Kisan dan kwallon, ta janyo zanga-zanga a garin Shagamu a ranar Litinin, zanga-zangar da ta kusan juyewa ta zama rikici inda wadansu matasa suka rufe manyan hanyoyin garin da tayoyi suka sanya musu wuta lamarin da ya sanya ’yan sandan kwantar da tarzomar yin harbi domin tarwatsa masu zanga-zangar.

A nan ma jama’a da dama suka samu raunuka hakan kuma ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutum guda a cikin masu zanga-zangar, Alhaji Inuwa Sarkin Shagamu, ya shaida wa Aminiya cewa zanga-zangar ta kazanta domin baya ga wadanda harsashin ’yan sandan kwantar da tarzomar ya shafa akwai wata dattijuwa da ke bara a bakin titi mai suna Gambo, wacce Allah Ya yi wa rasuwa sakamakon turmutsitsi lokacin da ’yan sandan suka koro masu zanga-zangar.

“A wannan turmutsitsin ne aka take dattijuwar sai daga baya aka gano ta rasu aka sanar mana, a ranar Litinin muka yi mata sutura muka binneta. A gaskiya wannan lamari ya tada hankalinmu,” inji shi.

Bayan zanga-zangar ce a yammacin ranar Litinin Babban Sufeton ’Yan sanda Najeriya, Muhammed Adamu ya bada umarnin janye lamarin da ofishin rundunar da ke Eleweron a Abeokuta zuwa ofishin Mataimakinsa da ke Onikan a Legas, ya ba Mataimakinsa AIG Ahmed Iliyasu, umarnin ya ci gaba da bincikar lamarin.

Haka zalika Babban Sufeton ’Yan sandan ya soke  jami’an rundunar ta musanman ta ZIS SARS a Jihar Ogun. Mai taimaka wa Babban Sufeton ’Yan sandan a bangaren binciken miyagun laifuffuka Peter OgunYonwon ne ya bayyana haka lokacin da ayarin jami’an ’yan sandan karkashin jagorancinsa da Gwamnan Jihar Ogun, Prince Dapo Abiodun, suka kai ziyara ta’aziyya ga iyayen marigayi dan kwallon a garin Shagamu, inda ya  ce, rundunar ta kori dan sandan mai mukamin sufeto da ake zargi da hannu a kisan dan kwallon, kuma tana bincikar ragowar ’yan sandan da lamarin ya shafa domin zuwa yanzu an kame dukkansu.