✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kisan gilla ga Jami’an Hukumar NDLEA

A kwanakin baya ne wadansu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka yi wa wadansu jami’an Hukumar Yaki da Tu’ammali da…

A kwanakin baya ne wadansu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka yi wa wadansu jami’an Hukumar Yaki da Tu’ammali da Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) hudu kisan gilla ta hanyar bude musu wuta.

Al’amarin ya faru ne a daidai Layin Ikaro da jami’an ke gudanar da sintiri a Karamar Hukumar Ifon Ese da ke Jihar Ondo.

Rahotanni sun nuna kimanin makonni uku ke nan da jami’an Hukumar NDLEA suka kai wani samame a wani yanki da ya yi kaunrin suna wajen yin mu’amala da miyagun kwayoyi inda suka yi nasarar kama wadanda ake zargi da laifi da dama kuma da lalata kwayoyi na miliyoyin Naira.

An ce maharan a kan babura suna dauke ne da bindigogi kirar AK-47, bayan sun kashe jami’an sun kuma kona motarsu kirar Toyota Hilud inda suka yi awon gaba da harsasai da muhimman takardu  ba tare da an kama ko an san ko su wane ne ba.

Jami’an Hukumar NDLEA hudu da maharan suka kashe su ne Abduljalal Mohammed mai mukamin (ASN II) da Wellington Eammanuel mai mukamin (SNA) da Magaji Aliyu mai mukamin (CAN) da kuma Mohammed Iliyasu.  Sai dai rahoto ya nuna cikon na biyar ya samu nasarar tserewa ba tare da an yi masa kwarzane ba.

Rahoton ya ce wadansu manoma ne suka ci karo da gawarwarkin jami’an da aka kashe. a yashe a wata gona kafin su sanar da jami’an tsaro.

Rahotanni sun ce maharan sun kai wannan hari ne don daukar fansa musamman ganin yadda jami’an NDLEA ke yawan takura musu wajen hana su cin karensu ba babbaka.

Hukumar NDLEA a Jihar Ondo dai ta sha alwashin kakkabe masu yin hulda da miyagun kwayoyi a  fadin jihar.  A watan Satumban bara, hukumar ta samu nasarar lalata kilo dubu 110 da 542 na tabar wiwi a gaban manyan jami’an hukumar ciki har da Gwamna Oluwarotimi Akeredolu.  Haka hukumar ta samu nasarar kama kilo dubu 851 na kwayar taramadol da kilo dubu 851 na sauran miyagun kwayoyoyi.  Hukumar ta gudanar da wannan samame ne a shirinta na yaki da mu’amala da miyagun kwayoyi da ta yi wa taken “Operation Ijo Oloogbo.”  Shirin dai yana karade kowane lungu da sako ciki har da gonakin da ake shuka wiwi da sauran miyagun kwayoyi.

Shugaban Hukumar NDLEA ta Jihar Ondo Haruna Dagara ya tabbatar da aukuwar wannan lamari.  Sai dai ya ce hukumarsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da yaki da masu tu’ammali da miyagun kwayoyi duk da karancin kayayyakin aikin da take fuskanta.

Ya ce wannan shi ne karon farko da aka kai musu irin wannan mummunan hari.

Dagara ya ce a kokarin da hukumarsa ke yi na kakkabe batagari a jihar, sun samu nasarar kama kilo dubu 30 da 618 na tabar wiwi da aka shuka a wata gona a garin Ipele da ke Karamar Hukumar Owo.

Ya ce a duk lokacin da hukumarsa ta kai wani sameme to suna sa ran za a iya kai musu hari don daukar fansa a kowane lokaci. A kan haka ne ya hori jami’ansa su kara yin taka-tsantsan a lokacin da suke gudanar da aikinsu. Ya ce duk da yake ana yawan kai musu hare-hare daga batagari musamman masu mu’amala da miyagun kwayoyi, hakan ba zai karya musu gwiwa ba.

A nan muna kira ga gwamnati ta gaggauta biyan hakkokin wadannan jami’ai na NDLEA da aka yi wa kisan gilla ga iyalansu.  Hakan zai karfafa wa sauran jami’an hukumar NDLEA gwiwa wajen ci gaba da aikinsu ba tare da nuna tsoro ko shakka ba.

A gaskiya ana yawan rasa jami’an tsaro a sassan kasar nan wadanda ke kokarin kare kasa da mutanen kasar.  Ana yawan rasa jami’an tsaron da ke yaki da ’yan kungiyar Boko Haram ko masu garkuwa da mutane da ’yan fashi da makami da masu fasa bututun mai da sauransu.

Ya dace gwamnati ta rika wadata irin wadannan jami’an tsaro da kayan aiki da suka hada da bindigogi da motoci da na’urorin sadarwa na zamani da sauransu. Hakan zai rage masu aikata laifuffuka da kuma rage yawan asarar rayukan jami’an tsaron.

Muna fata jami’an tsaro za su tsananta bincike don zakulo wadanda suka aikata wannan mummunan ta’addanci don su fuskanci shari’a.