✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kisan Janar Alkali: ’Yan sandan Filato na neman mutum 13 ruwa a jallo

Rundunar ’Yan sandan Jihar Filato ta fitar da sanarwar neman wadansu mutum 13 ruwa a jallo bisa zarginsu da hannu wajen bacewa da kuma kashe…

Rundunar ’Yan sandan Jihar Filato ta fitar da sanarwar neman wadansu mutum 13 ruwa a jallo bisa zarginsu da hannu wajen bacewa da kuma kashe Manjo Janar Idris Alkali (mai ritaya).

Rundunar ta fitar da sanarwa ne ta hannun Kakakinta, DSP Tyopeb Terna a jiya Alhamis. Sanarwar ta ce bisa umarnin Kwamshinan ’Yan sandan Jihar ne rundunar ta sanar da jama’a cewa an yanzu tana neman wadannan mutane 11 da bincikenta ya gano suna da hannu wajen kashe Janar Alkali.

Mutane da rundunar take nema ruwa a jallo sun hada da  Kannan Nyam da Solomon Gyang Jang da Dustine (babu sunan mahaifi) da Dung Deme da Gyang Murrak da Da Chuwang Samuel da Nyam Samuel da kuma Dung Gbeh. Sauran wadanda ake neman sun hada da Daddy Dogo da James Dung da Gyang Dung da Jay Boy da kuma Gyang (babu sunan mahaifi).

Rundunar ta ce wadanda ake neman dukansu maza ne kuma mazauna kauyen Dwei da ke Gundumar Du a Karamar Hukumar Jos ta Kudu, in ban da Gyang wanda ba a kai ga gano sunan mahaifinsa ba da ke da zaune a kauyen Guchwet a Gundumar Shen a Karamar Hukumar Jos ta Kudu.

“Duk wanda ya ga wadanda ake neman  sai ya tuntubi ofishin ’yan sanda mafi kusa ko kuma ya kira wadannan lambobi kamar haka: 07059473022 ko 08038907662 ko 08075391844 ko kuma 09053872296,” inji Rundunar ’Yan Sandan Filato.