✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kisan Kudirat Abiola: Gwamnatin Legas ta daukaka kara

Gwamnatin Jihar Legas ta shigar da kara kotun koli tana kalubalantar hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke na wanke Manjo Hamza Almustapha da Lateef…

Gwamnatin Jihar Legas ta shigar da kara kotun koli tana kalubalantar hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke na wanke Manjo Hamza Almustapha da Lateef Shofolahan kan zargin kashe Alhaja Kudirat Abiola.
A watan da ya gabata ne kotun daukaka kara ta yi watsi da hukuncin da babbar kotun Lagos ta yanke na zartar da hukuncin kisa a kan Manjo Almustapha da Shofolahan.
A wani taron manema labarai ta gwamnatin ta kira a Alausa da ke Ikeja, Atone Janar na jihar kuma kwamshinan shari’a, Ade Ipaye ya ce gwamnatin jihar ta shigar da kara kotun koli tun ranar Litinin din da ta gabata tana kalubalantar hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke.
Ya ce, “Ma’aikatar shari’a ta Jihar Legas ta mika takardun daukaka kara don kalubalantar hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke kan shari’ar Lateef Shofolahan da gwamnatin jihar da kuma Almustapha da gwamnatin jihar”.
Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta yi nazarin hukuncin da kotin daukaka kara ta yanke inda aka  lura cewa akwai dalilan daukaka kara. “Bayan da muka yi nazarin hukuncin da alkalan kotun suka yanke sai muka lura cewa akwai dalilan da suka sa mu daukaka kara a kotun koli kuma muna sa ran kotun za ta yi amfani da wadannan dalilai’. Inji shi.
Atone-janar ya kara da cewa matakin da gwamnatin jihar ta dauka zai kawo karshen kiki-kakan da ake ta samu kuma iyalai da wadanda ake zargi da kuma mutanen gari za su kasance ba a hana su damar da kundin dokokin Najeriya ya bayar ba na damar da za su amfani da ita domin samun adalci.
Ya kara da cewa gwamnatin jihar ta himmatu wajen tabbatar da an sami jama’a masu bin doka da oda da kuma samun baki da za su  rayu su yi aiki tare da cimma burin su a muhalli mai tabbatacen tsaro da kwanciyar hankali.