✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kishin matasa ya sanya ni shiga siyasa  – Salisu Wake Up

Salisu Muhammad, wanda ake wa lakani da Wake Up Katsina Youth, daya ne daga cikin matasan ’yan siyasa da suka amsa kiran matasa su shiga…

Salisu Muhammad, wanda ake wa lakani da Wake Up Katsina Youth, daya ne daga cikin matasan ’yan siyasa da suka amsa kiran matasa su shiga siyasa, inda yanzu haka yake takarar Majalisar Wakilai a Jam’iyyar Accord a Katsina. Aminiya ta tattauna da shi kamar haka:

 

Mene ne takaitacen tarihinka?

Sunana Salisu Muhammad, an haufe ni a Unguwar Kofar Kaura, Katsina. Na yi firamare da sakandare da karatun Difloma a garin Katsina. Kuma na yi karatun allo da Islamiya a garin Katsina. A yanzu haka na yi digiri na daya da na biyu a kan Hulda da Kasashen Waje da kuma Diplomasiyyar Duniya.

Ni ne matashin da na kalubalanci tsohon Gwamnan Jihar Katsina ta hanyar tura korafi a kan matasa 3,500 da Gwamna Shema ya kora daga aiki. Ni ne na nuna rashin amincewata ta hanyar rubuta korafi a kan kudin Jami’ar Umaru Musa ’Yar’aduwa (UMYU) da ya kara har ya zarce na dukan jami’o’in Arewa tsada. Ni ne jami’in gudanarwa na Kungiyar Matasa ta ABM a Karamar Hukumar Katsina. Na jagoranci zanga-zangar lumana a lokuta da yawa, kamar lokacin da dillalan man fetur suka boye man. Ni ne Sakataren Kungiyar Matasa da ke kula da muhalli kuma Sakataren Kungiyar YESJUF kuma Shugaban Katsina State Social Media Forum.

Na kalubalanci Shugaban Hukumar Sibil Difens na kasa mai ci yanzu tare da Shugaban  Hukumar Daidaiton Ma’aikata ta kasa a kan kin bin dokokin daukar aiki.

 

Me ya ba ka kwarin gwiwa shiga takara a matsayinka na matashi?

Na samu kwarin gwiwar fitowa takara ce a kan yadda na ga matasa ne suka yi ruwa suka yi tsaki don ganin wadansu sun samu nasara a zaben 2015. Amma kuma matasan da suka yi waccan tsayuwar daka don tabbatar da wancan nasara, su ne ake yi wa kallon uku kwabo. Kuma lokaci ya yi da matasa za su daina zama a majalisun hira suna zagin ’yan siyasa. Matasa ya kamata su dauki salon dawowa da duk wani dan siyasa da yake rawa da bazarsu sannan yana yi wa matasan kallon uku kwabo.

 

A wace jam’iyya kake takara kuma wane mukami kake nema?

Ina takara ce a Jam’iyyar ACCORD kuma ina takarar dan Majalisar Wakilai a mazabar Katsina ta Tsakiya.

 

Mene ne kudirinka, idan ka samu nasara?

Za mu yi doka a kan gyara albashin malaman makarantar firamare da na sakandare. Za mu tabbatar da an yi amfani da ka’idojin daukar aikin gwamnati ba irin yadda alfarma ta yi kaka-gida cikin daukar aiki ba.

Za mu gayyato kungiyoyin sa-kai (NGOs) domin su shiga cikin batun gurbatar muhalli a Arewa. Sannan mu zuba ido a kan kudaden tallafi na duniya da ake samu domin kare muhalli (Great Green World) da sauransu.

Za mu tabbatar da cewa kowace rumfar zabe daga rumfunanmu 281 ta ba da wakili da za mu rika zama kafin mu tura bukatunmu a kasafin-kudi.

Za mu yi doka a kan shirin Inshorar Lafiya ta kewaya cikin kauye da birni.

 

Ta yaya kake ganin za ka bambanta da sauran ’yan takara?

Za mu rika kai bukatun al’umma ba bukatun da muke zaton suna so ba. Za mu kula mu ga mene ne suka ce sun amince mu je mu gabatar. Ba za mu yi amfani da kudin al’umma ba wajen yi wa wadansu tsiraru kyauta.