✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kiwon lafiya ta fuskar sana’o’inmu

Waxanne irin haxurra ke tattare da sana’o’in hannu? Ni aikin walda nake yi. Wace shawara za a ba ni domin kare lafiyata? Don an ce…

Waxanne irin haxurra ke tattare da sana’o’in hannu? Ni aikin walda nake yi. Wace shawara za a ba ni domin kare lafiyata? Don an ce ba mu tsufa da idonmu qalau. Shekaruna ba su wuce ashirin da biyu ba.

Daga I. M. Abubakar, Kano
Sai mai cewa: Ni kuma ina aikin wahala ne. Wane irin abinci da magani ya kamata na riqa ci da sha, don kada na tsufa gajiya ta tashi?
Daga Aliyu Y. Jigawa
Amsa: A haqiqanin gaskiya ba sana’ar da ba ta qunshe da gajiya da haxurra ga lafiyarmu sai dai wata ta fi wata. A aikin walda ba idanu ne kaxai suke shan wahala ba ga mai walda, duk inda tartsatsin narkakken qarfe ko dalma ta tava a jikinka akwai illa ko dai ta quna ko wani abu daban. Dole ke nan mai walda ya tanadi kayan da za su rufe jiki gaba-xaya, domin kiyaye waxannan, muhimmi daga ciki shi ne gilashin rufe fuska gaba xaya ba tabarau na ido kaxai ba. Kuma ba qanshin gaskiya a ce wai ba zai tsufa da idonsa qalau ba, ko gajiyar sana’a na tashi.
Sauran misalan da zan ba ku a xaya vangaren tambayar, na irin wahalhalun da ke tattare da sana’o’inmu sun haxa da:
Noma: Wanda ake ce wa naduqe tsohon ciniki. Wataqila saboda wahalarsa ce a yanzu yake nema ya zama tarihi. Matsalolinsa sun haxa da yawan ciwon baya, kantar hannu, shiga haxarin cizon qwari da dabbobi irinsu kunama da maciji da sauransu. Sauran su ne saurin samun ciwon qaba, ko kwasar qwayoyin cuta a kududdufai idan an je wanke jiki, qwayoyi irin masu kawo tsargiya, kurkunu, dundumi da sauransu. Noman zamani da ake yi ta hanyar na’urori kamar motar huxa da ta shuka da ta girbi duk ba su tattare da irin wannan haxari.
Kiwo: Shi ma xan uwan noma ne kuma duk haxarin noma zai iya shiga haxarin kiwo. Bugu da qari kuma ga haxarin kamuwa da cututtukan dabbobi irinsu ciwon barci ko sammore, wanda qudan tsando ke kawowa, ko tarin TB na dabbobi da sauransu.
Su: Masunta suna cikin haxarin lumewa cikin ruwa ko shan gurvataccen ruwa mai qwayoyin cuta da kamuwa da qwayoyin cuta irinsu tsargiya.
Jima: A yanzu da yake kamfanonin jima sun yi qaranci, an xan rage samun cututtukan da ke faruwa sanadin wannan matsala. Yawanci qwayoyin cuta ne ke taruwa a kan fata idan an zo wanke su a kwashe su. A inda kamfanunnukan fata suka rage a kodayaushe magudanan wurin ba sa rabo da ruwa mai wari wanda ke xauke da nau’ukan qwayoyin cuta iri-iri, waxanda kan iya shiga ruwan gari ta fasassun bututu, a samu cututtukan ruwa irinsu amai da gudawa.
Rini: Marina suna xaya daga cikin mutanen da suka fi samun ciwon daji na mafitsara da dangoginsu, sakamakon sinadaran haxi na yin rini. Wato shi tirin da ake jiqawa wasu masana sun tabbatar yana iya kawo ciwon daji.
Qira: Maqera kuma sun fi shiga haxarin raunuka da qarafuna da quna daga garwashin wuta.
Tuqi: A yanzu wannan sana’a ita ce za a ce ta fi kowace sana’a haxarin cutarwa da ma rasa rayuka, domin nasu kullum ne. Direbobi ko da ba ma na sana’a ba, musamman masu tuqin nesa sun fi kowa samun karaya da buguwa da sauran matsaloli na haxarurrukan qarfe irinsu mutuwar wani vari na jiki da sauransu.
Sana’ar wasanni: Duk da cewa wasanni na motsa jiki suna xaya daga cikin sana’o’i masu gyara jiki da qara lafiya, da wuya a samu cikakken xan wasan da bai tava samun karaya ko targaxe ba.
Gini Da Injiniyanci: Magina da injiniyoyi suna xaya daga cikin mutane masu samun haxurra su ma na buguwa da cutuwa daga injina ko matsalar kunne idan inji yana da qara. Shanyewar sashen jiki sakamakon faxowa daga sama ko kuma wani abu ya faxo wa mutum daga sama kan faru. Ruwan fenti, wannan yana da sindarin dalma da zai iya kawo illa ga lafiya.
Sayar da Abinci: Masu sayar da abubuwan ci da na sha kamar masu masu qosai da ma masu dafa abincin sayarwa a gida waxanda suke amfani da murhu, suna xaya daga cikin waxanda hayaqin itace ke wa illa a huhu. An qiyasta cewa bayan taba sigari, masu girki a gaban murhu su ne kan gaba wajen matsalolin huhu. Ba nan hayaqin ya tsaya ba, yakan yi illa a ido ma.
Kanikanci: Yawanci bakanikai ba wai datti ba ne yake sa jikinsu da kayansu baqi, baqin mai ne kawai. Suna cikin haxarin samun dusashewar fata dalilin wannan mai, saboda ba kowane sabulu ba ne ke iya wanke shi amma ban da duhun, ba wata illa yake ga ita fatar ba. Sai dai duk da haka yana da kyau su ma su riqa rufe duka fatar tasu da dogayen kaya da sanya safar roba a hannayensu, domin da dama haka suke cin abinci da hannun ba tare da sun wanke su sosai ba, tunda duk inda aka samu maiqo za a samu qwayoyin cuta.
Wanki da guga: Masu sana’ar wankau su kuma sun fi kowa samun matsalar cin ruwa a fata saboda yawan hulxa da ruwa, sai kuma cin fata da sabulai ko omo kan yi.
Ma’aikatan Ofis da ’Yan kasuwa: Masu iya magana suka ce wai ‘zama wuri xaya tsautsayi inji kifi.’ Wannan tsautsayi ba kan kifi kawai ya tsaya ba, waxanda suke da sana’ar zama wuri guda na tsawon lokaci kamar masu aikin ofis da yawa-yawan ’yan kasuwa su kuma sun fi kowa shiga haxarin kamuwa da cututtukan qiba da na hawan jini da cututtukan zuciya saboda rashin kazar-kazar, saboda ban da yawan zaman kuma kusan sun fi kowa son cin ‘daxi.’
Aikin lafiya: A qarshe mu ma ba a bar mu a baya ba wajen samun matsalolin lafiya a wuraren aiki. Mu ma namu haxurran ba qanana ba ne. Duk wanda ya zo da qwayoyin cuta, yawanci a kanmu yake baje su, kamar na tarin fuka da mura, ban da haxarin kamuwa da cututtukan cikin jini irinsu qanjamau da ciwon hanta da yawanci masu fixa ko xibar jini kan samu. Masu gajen haquri a dangin marasa lafiya a kanmu suke huce haushinsu wajen faxa da masu jiyya har ma da bugun kawo wuqa, duk da cewa wasunmu mu ma muna da hannu wajen jawo faxa.
Waxannan misalai ne kawai, domin ba a tavo wasu da dama ba irin masu sana’ar aikin ba-haya ba da masu sayar da fetur. Kowa idan ya tuna sana’a zai iya fito da haxarin da ke tattare da ita. A taqaice dai duk inda ka duba za ka ga akwai haxari ga lafiya tattare da kowace sana’a, sai dai kawai a riqa xaukar matakan kariya daga duk abubuwan da aka zayyana ga kowace sana’a, wanda mun san masu karatun wannan shafi yanzu qwararru ne a wannan vangare. Mai aikin qarfi zai iya shan maganin ciwon jiki irinsu panadol amma ban da masu sa nacin sha da maye irinsu tramol.