✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko Adam A. Zango zai yi auren huce haushi yau?

Ko Adam A Zango zai yi auren huce haushi? Wannan ita ce tambayar da jama’a suka rika yi sakamakon samun labarin jarumin zai kara aure…

Ko Adam A Zango zai yi auren huce haushi? Wannan ita ce tambayar da jama’a suka rika yi sakamakon samun labarin jarumin zai kara aure makonni kadan bayan an fasa aurensa da Asiya Ahmad, kanwar Samira Ahmad matar T.Y Shaba.
A yanzu dai an baza jita-jitar jarumin zai yi auren huce haushi ne kasancewar jarumin ya zargi dangin tsohuwar jaruma Samira Ahmad da hana shi auren Asiya.
Wata majiya ta bayyana jarumin ya kasance cikin takaicin rashin auren Asiya, saboda ya nuna mata matsananciyar soyayya, kuma hakan ne ta sanya ya nuna wa dangin Asiya yana da farin jini, shi ne yau za a daura masa aure da ‘yar babban gida.
Da Aminiya ta tambayi jarumin kan wannan jita-jitar sai ya ce: “Matar mutum kabarinsa, kuma duk yadda mutum ya kai da son mallakar abu idan ba rabonsa ba ne ba zai same shi ba, hakan duk yadda kake da tsanar abu idan zai kasance tare da kai sai ya kasance. Don haka wannan jita-jita ce kawai da ba za a raba ’yan Adam da ita ba. Ni dai abin da nake roko shi ne mutane su taya ni da addu’ar zaman lafiya cikin wannan auren.”
 A yau Juma’a 14 ga watan Yuni, 2013 za a daura auren shahararren jarumin da Nana Maryam Abdullahi Yola, a Lugbe da ke Abuja.
Za a daura auren ne da misalin karfe 1:30 a masallacin Juma’a da ke Lugbe.
Nana Maryam za ta kasance matar jarumin ta uku.
Idan hali ya yi a mako mai zuwa za mu gabatar muku da yadda bikin ya gudana.