✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko akwai maganin minshari?

Ni dai ina da mata mai yawan gwarti idan tana barci, kuma tana damuna. Me ke kawo shi? Kuma yana da magani? Amsa: Hakika mutane…

Ni dai ina da mata mai yawan gwarti idan tana barci, kuma tana damuna. Me ke kawo shi? Kuma yana da magani?

Amsa: Hakika mutane da dama ba za su san girman matsalar minshari ba sai wani na kusa da su a wurin kwanciya ya fara samun matsalar. Tabbas ko ba a tambaya ba mutane da dama sukan yi fama da wannan matsalar ta gwarti yayin barci. Hasali ma an fi samun wannan korafi a tsakanin ma’aurata kamar kai mai tambayar, kuma yakan iya jefa aure cikin hadari musamman ma idan daya yana yi, dayan kuma ba ya yi. A wasu lokutan kuma a tsakanin abokai ko ’yan uwa masu kwana daki daya a kan samu korafin.

Duk da cewa kowane dan Adam zai iya yin minshari yayin barci, marar kara sosai, amma minshari mai kara sosai mai cika daki ya fi yawa a mutane masu kiba ne, mata ne ko maza. Domin an kiyasta cewa fiye da rabin mutane masu kiba suna fama da wannan larura. Kai wasu lokutan ma har yara masu kiba kan yi. Kamar yadda za a rika gani a kusan yawancin rubutunmu, shan barasa da zukar hayakin sigari kan iya sa kowace irin matsala ta likitanci shi ya sa akan samu a mutane masu shan sigari ko barasa, ko da ba su da kiba. A wasu lokuta kuma toshewar hanyoyin numfashi kamar mura ko ciwon asma ma za su iya kawo wannan matsala.

Minshari kan faru ta sanadin abubuwa da dama, kamar karkarwar tantanin makwallato a lokacin barci (domin kiba da yawan zukar taba sigari kan sa wannan tantani ya sakwarkwace), ko rashin iya wucewar iska zuwa huhu saboda kiba ta yi yawa a makogwaro ko mura ko kuma mutum ya kwanta ba daidai ba, ta yadda harshensa ko kashin muka-muki kan toshe hanyar numfashin.

Minshari kan iya sa numfashi ya rika daukewa na wani lokaci, wanda hakan kan iya sa mutum yawan tashi cikin barci. Wannan yawan tashi kuma kan sa mutum yawan kasala da rana ko yawan barci yayin aiki.

Sauran hadarurrukan minshari sun hada da hadarin samun bugun zuciya.

Akwai ma alaka tsakanin masu ciwon minshari da ciwon mutuwar barin jiki wanda shi ne kiba.

Hanyoyin kiyaye karkarwar tantanin makwallato dai ita ce ta barin shan sigari, sai rage kiba. Wadannan kan sa makogwaron ya washe, sai kuma kiyaye yanayin kwanciya, domin kwanciya a gadon baya alal misali, kan sa harshe ya fada baya kusa da makogwaro ya toshe hanyar numfashi, don haka dole a kula da kwanciya da gefen jiki kawai. Duk da haka kuma, ga wanda duk ya dauki wadancan matakai amma minsharinsa ya ki tafiya, akwai ’yan dabaru da akan yi a asibiti na rage matsalar ta saitawa ko gyara yanayin tantani ko na makogwaro. Akwai dabaru iri-iri wadanda likitocin makogaro za su iya yi tun daga samar da wani madaurin haba mai kama da linzami, wanda zai saisaita muka-muki yayin barci, har zuwa tiyata. A irin wannan tiyata, bayan an kashe makogwaron da abin fesawa na kashe zogi, akan yi allura, ko amfani da hasken wutar laser a rage teba a makoshin ko gyara tantanin ko ma duk abin da ya toshe makogwaron.

A mafi yawan lokuta minsharin mai barci yakan sa wanda ke dakin shi ma ya kasa barci. A irin wannan yanayi idan an kasa magance minshari ta wadancan hanyoyi da aka yi bayani a sama, ko idan mai minsharin ya ki daukar daya daga cikin matakan, sai dole wanda aka dama din ke nan ya fara daukar matakai a karan kansa domin ganin ya samun sa’ida cikin barci. Zai iya sayen abubuwan toshe kunne (earplug) misali don kada minsharin ya hana shi barci. Kai wadansu ma abin har sa su yake su raba daki, wanda ba a fata. Amma idan ta kama a raba dakin domin a samu cikakkiyar natsuwa yayin barci sai a raba din.

 Me ke sa yawan gajiya da saurin barci ba tare da wani aiki mai tsanani ba?

Daga MK Kaura

Amsa: To ko kai ma kana yawan samun minshari da dare ne, domin yana daga cikin manyan abubuwan da kan sa kasala da rana saboda rashin isasshen barci da yakan sa da dare kamar yadda muka zayyana a sama.

Akwai kuma sauran dalilai na wasu cututtuka kamar su ciwon suga. Idan kai ka kasa gano dalili za aka iya neman taimakon likita kai-tsaye, ya aunaka ya yi maka gwaje-gwaje a gani ko akwai wani ciwo da ba ka san da shi ba.

Ni kuma idan ina karatu bayan minti daya ko biyu sai zafi da hawaye. Akwai matsala?

Daga Idris Muhammad

Amsa: Da alama kai bako ne a shafin nan. Akwai matsala mana, sai likitan ido ya duba idon.

Ina fama da ciwon shakuwa. Idan na fara sai na ji kirjina na mini zafi tare da cikina. Ko matsala ce?

Daga Bala Malam-Madori

Amsa: Eh, matsala ce babba yawan shakuwa hade da zafin ciki. Don haka kada ka yi kasa a gwiwa wajen zuwa a binciki dalili domin a yi maganinsa da wuri.

Da yake ina da infection a kafa na tsawon shekara hudu maganin da nake sha wajen rage radadi yana ba ni wahala amma ina jin saukin zafin sosai. Yaya zan yi?

Daga U.A Kalaba

Amsa: Infection tsawon shekara hudu? Haba yallabai, babu asibiti a Kalaba ne? Ka san da cewa kuwa tsohon ciwo irin wannan zai iya yin ajalinka? Ka daure ka nemi likita a asibitin kashi idan kana so ka warke sarai.

Fatar fuskata iri biyu ce domin daga wurin idanuna ta yi baki mutane ma sun dauka shafe-shafe ne. akwai magani?

Daga Hafsat A.

Amsa: Wasu cututtukan fatar haka suke farawa da dabbare-dabbare a fuska. Ki je tunda wuri ki ga likitan fata, ya gani ya ba ki magani.