✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko ‘Da Kai Zan Gana’ zai bambanta da sauran fina-finan 2 Effect?

A makon jiya ne kamfanin shirya fim na 2 Effect Empire ya kammala daukar fim dinsa mai suna ‘Da Kai Zan Gana’.An dauki fim din…

Daga hagu Yakubu, Rahama, Zaharaddin da kuma Sani yayin daukar fim din ‘Da Kai Zan Gana’A makon jiya ne kamfanin shirya fim na 2 Effect Empire ya kammala daukar fim dinsa mai suna ‘Da Kai Zan Gana’.
An dauki fim din ne a Kaduna da kuma Abuja.
Wannan ne fim na farko da Sani Danja da Yakubu Mohammed ba su tsara labari ko ba da umarni ko shiryawa ba. Inda Ibrahim Birniwa ya rubuta hade da tsarawa, Naziru dan Hajiya ya shirya, Sadik M. Mafia kuma ya ba da umarni.  
‘Da Kai Zan Gana’ labari ne a kan Abdallah (Sani Musa Danja) da kannensa Faruk (Yakubu Mohammed) da Mudassir (Zaharaddin Sani). Labarin ya samo asali ne lokacin da Abdallah ya kuduri niyyar aure, amma sai wani abin takaici ya faru, domin wani abu ya gifta tsakanin kannensa da budurwarsa (Rahma Sadau). Da farko ta hadu da Faruk a hanya bayan ta baro kauyensu, har ya yi mata fyade. Bayan ta shigo gari har ta samu wurin zama, sai ta hadu da Mudassir, daga baya ya hilace ta har ya sanya mata magani cikin abin sha daga karshe ya sadu da ita.
Bayan Abdallah ya kawo ta gida ne ta hadu da kannensa, yanayin yadda kannensa da budurwarsa suka yi ne ya nuna lallai akwai lauje cikin nadi, wanda hakan ya sa ya shiga damuwa. Ya yi ta tambayarsu abin da yake faru suka ki gaya masa, bayan tafiya ta yi tafiya ne aka gano sirrin da yake boye, inda mahaifiyarsu ta rika kuka. Haka ya sanya ya fasa aurenta hade da yin alla-wadai da ita.
Bayan an yi waiwaye ne sai aka gano ashe budurwar tasa ta bar kauye ne don mahaifiyarta ta ce ga wanda ya dace ta aura.
A karshe an yi ta ba shi hakuri har ya yarda, sai aka yanke shawarar a koma wurin malamai a yi tambaya shi ko aure ya halarta tsakaninsu? Idan kun kalli fim din za ku ga fatawar da za bayar.
Da wakilinmu ya tuntubi furodusan fim din Naziru dan Hajiya sai ya ce, “fim ne da ke nuna duk wanda ya bijire wa umarnin iyayensa ba zai ga daidai ba, ya kuma nuna idan iyayenka suka umarce ka da yin abu to ba za su ba ka umarnin abin da zai cutar da kai ba. A lokacin da za ta bar kauye ne mahaifiyarta ta ce idan ta tafi ba da yawunta ba, sai ta ce ta yarda, a karshe ta tsinci kanta cikin mawuyacin hali.”
 Jarumin fim din Yakubu Mohammed ya ce wannan fim din ya bambanta da sauran fina-finansu, domin shi da Sani jarumai suka fito.
Shi kuma Sani Danja ya ce rawar da ya taka a fim din ta burge shi, jarumar fim din kuma ta yi kokari sosai.
Sauran ’yan wasan sun hada da Ladidi Fagge, Rahama Sadau, Maimuna Wata Yarinya, Hadiza Gabon da sauransu.