✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko ‘Gidan Aure’ zai kasance waraka ga matsalolin ma’aurata?

A makon jiya ne kamfanin Songs and Film Limited da ke Abuja ya kammala daukar fim din ‘Gidan Aure’.Fim din ‘Gidan Aure’ labari ne da…

A makon jiya ne kamfanin Songs and Film Limited da ke Abuja ya kammala daukar fim din ‘Gidan Aure’.
Fim din ‘Gidan Aure’ labari ne da ya shafi ma’aurata, inda aka nuna kananan matsaloli da ke addabar ma’aurata.
Labarin ya zo da fuska biyu. Fuska ta farko ta shafi gidan Kabiru (Sadik Ahmad) da matarsa Maryam (Fatima Yusuf). Maryam tana da son abin duniya har ta kai ko da mijinta zai yi tarayya da ita sai sun yi ciniki ya biya.
Sai kuma fuska ta biyu, wato gidan Misbahu (Ali Nuhu) da matarsa Basma (Nafisat Abdullahi). Suna matukar son junansu sai dai kuma Basma ba ta iya girki ba. Shi kuma Misbahu na da matsala biyu, na farko ba ya iya biya wa matarsa bukatar kwanciya, idan kuma yana barci sai ya rika minshari. Amma sakamakon matsanancin son da suke yi wa junansu sai suka yi kawaici ba tare da sun tattauna matsalolin ba. Wadannan matsalolin ne suka haddasa musu fitina a gida. Ya daina cin abincin matarsa sai da ya fita ya saya a waje, inda kuma daga baya ta gane.
Malam Hashim (Rabi’u Rikadawa) ya taka muhimmiyar rawa, inda ya fito a matsayin malami da ke warware matsalar gidan Kabiru da matarsa da kuma gidan Misbahu da matarsa.
Da aka tambayi wanda ya dauki nauyin fim din ‘Gidan Aure’, Bashir Datti kan abin da zai ce a kan fim din sai ya ce: “Abin da ya fi burge ni dangane wannan fim din shi ne, yadda aka tsara labarin da kuma yadda ma’aurata za su fa’idantu kan muhimmancin tattaunawa da kuma kyakkyawar fahimta a tsakaninsu. An kuma bayyana yadda karamar matsala idan ba a shawo kanta ba takan zama babba har ta kai rabuwar aure.”
Jarumin fim din Ali Nuhu ya ce ya gamsu da rawar da ya taka a fim din, musamman da zai zama fitalar da zai haskaka wa ma’aurata wadansu hanyoyi don su gane wadansu matsaloli da suke fuskanta.
Ya ce: “Akwai matsaloli masu yawa cike da rayuwar aure, amma sai ka samu ba a tattauna su, a wannan fim din an bayyana hakkokin miji a kan matarsa da kuma na mata a kan miji. An kuma yin bayanin yadda ma’aurata za su shawo kan matsalar da ke ci musu tuwo a kwarya ba tare da al’amarin ya fita waje ba.”
Yakubu M Kumo da Habeeb Mu’azu ne suka rubuta labarin fim din. Kamal S. Alkali ya ba da umarni.
‘Yan wasan sun hada da: Ali Nuhu da Sadik Ahmad da Fatima Yusuf da Nafisa Abdullahi da Ladidi Fagge da Rabi’u Rikadawa da sauransu.
Sai dai abin tambaya a nan shi ne ko fim din ‘Gidan Aure’ zai zama waraka ga matsalolin ma’aurata?