✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko haramta amsar sarautar gargajiya ga ma’aikatan gwamnati ya dace?1

An dade ana ta kai-komo domin ganin an yi dokar da za ta haramta wa jami’an gwamnati amsar sarautun gargajiya a lokacin da suke kan…

An dade ana ta kai-komo domin ganin an yi dokar da za ta haramta wa jami’an gwamnati amsar sarautun gargajiya a lokacin da suke kan aiki. Abin tambaya a nan shi ne, shin ko ya dace a yi irin wannan doka? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu nan kamar haka:

Bai kamata a ba ma’aikata sarauta ba – Isa Teacher

Malam Isa Muhammad Teacher: “Bai wa ma’aikatan gwamnati sarauta bai dace ba. Kamata ya yi in za a ba su, a bari sai mutum ya bar aiki. Duk wanda ka ga an ba shi sarauta, kudi ya kasha; ba don Allah ake ba shi ba. Ka ga haka yakan sa mutum ya debi kudin gwamnati ko na jama’a ya bayar a ba shi sarauta. Misali, ko wanda a gidansu ya ga ji sarauta ne, idan ka lura muddin bai da kudi, sarautar tana iya barin gidansu, a kai wani gida daban da ba su da gado; a ba su sarautar saboda kudi.”