✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko kirkiro da masarautu a Najeriya zai kawo ci gaba ne ko rarraba kawunan alumma?

Tun bayan kirkiro sababbin masarautu guda 4 da Gwamantin Jihar Kano ta yi, ya haifar da cece-kuce a tsakanin al’umma, inda kowa ke bayyana ra’ayoyinsa…

Tun bayan kirkiro sababbin masarautu guda 4 da Gwamantin Jihar Kano ta yi, ya haifar da cece-kuce a tsakanin al’umma, inda kowa ke bayyana ra’ayoyinsa mabambanta, Wakilan Aminiya ta jiyo ta bakin wasu daga cikin jama’a a kan wannan lamarin,wasu na cewa karin ya yi daidai, inda wasu kuma ke yin Allah wadai da hakan.

 

Babu wani ci gaba a kirkiro sababbin masarautu –Fatima Abubakar (Bintu)

Daga Ahmed Garba Mohammed,Kaduna

Fatima Abubakar da aka fi sani da Bintu ta ce, ci gaba da kirkiro sababbin masarautu da ake yi  hakan ba zai haifar da da mai ido ba.  Dalilin fadin haka kuwa shi ne, idan aka kirkiro da sabuwar masarauta to takan dusashe karsashin wacce ake da ita tun da farko musamman wadanda suke nan tun kaka da kakanni.

Sannan ba karamin kudi ake kashewa wajen kirkiro kowace masarauta ba, in kuwa haka ne me zai sa ba za a yi amfani da kudin wajen inganta wadanda ake da su a kasa tun da farko ba.

Don haka ban ga dalilin a rika kirkiro da sababbin masarautu babu gaira, babu dalili ba.

 

Kirkiro sababbin Masarautu zai kawo ci gaba – Abdullahi Lili Ajiyan Pantami

Daga Rabilu Abubakar, Gombe

Ra’ayi na akan kirkiro da sababbin masarautu a kasar nan, zai kawo cin gaban al’umma, domin al’ummar karuwa take kuma dangantaka ma karuwa take.

Wasu za su iya danganta kirkiro sababbin Masarautun Kano da siyasa, kuma ba siyasa ba ne, ci gaba ne ya kawo hakan.

Ya ya ba wa  Gwamnan Kano bisa  Kirkiro sababbin masarautun  da yayi a jihar , domin zai kawo ci gaba.

 

Ba zai kawo ci gaba ba – Muhamamd Sani Wudil

Daga Lubabatu I. Garba, Kano

Wannan kirkiro da masarautu da aka yi ba zai kawo wani ci gaba ba, domin ba masarautu mutane ke bukata ba, akwai abubuwa masu yawa da suka dami a’lumma kamar harkar lafya da sauransu. Haka kuma idan aka dauki batun kudin gudanar da masarautun wannan wani nauyi ne da zai kara hawa kan gwamnati.

 

Karin masarautu alheri ne – Fatima Abdullahi

Daga Ahmed Garba Mohammed a Kaduna

“A nawa ra’ayin ci gaba da kirkiro da sababbin masarautu daga lokaci zuwa lokaci  hakan ya dace kuma alheri ne, don hakan yana kawo ci gaba musamman ga yankin da abin ya shafa. Da zarar an sake kirkiro wata sabuwar masarauta, za ga ka ana samun ci gaba a fannoni da dama. Saboda haka ina goyon bayan wannan tsari 100 bisa 100.

 

Kirkiro Sababbin Masarautu ba zai rarraba kan al’umma ba–Dalhatu El-Nafaty

Daga Rabilu Abubakar, Gombe

Ya ce shi a shawararsa yana ganin kirkiro da karin sababbin masarautu a kasar nan alheri ne, domin zai rage wa jama’a wahalhalu a lokacin bikin sallah.

Ya ce ko a Gombe an taba yi inda aka mayar da duk sarakunan masu daraja ta daya, kuma ko da an rarraba masarautun ai dole akwai babba ko da duka darajar su daya ne.

Ya kuma ce nesa ne ta zo kusa jama’a, kuma sun samu sauki, idan ba ka da kudin mota na zuwa cikin gari don kallon Sarki sai ka tsaya a garin ku ka kalli Sarkin ku.

 

Zai kawo rarrabuwar kai – Auwal Abdullahi Sakkwato

Daga Muhammad Aminu Ahmad

Gaskiya kirkiro Karin masarautu a Kasar nan, a nawa ra’ayin za’a samu matsala sosai, babu wani cigaba da zai kawo illa ya sake raba kawunan alumma. Domin ko wanda akayi a kano, shima siyasa ce, tasa akayi hakan, zama da masaruta daya ce,babban abu ne da zai kawo hadin kai da Kara martaba sarkin.

Kuma a samu jiha da sarki daya mai fada aji, shine abin da jama’a ke so, amma ace an raba jiha daya an yi mata sarakuna har biyar ai, bai dace ba.