✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko Kotun Duniya aka je  Atiku da PDP za su sha kasa– APC

Shugaban Jam’iyyar APC ta Kasa, Kwamared Adams Oshiomhole ya ce ko Kotun Duniya aka je APC za ta yi wa PDP da dan takararta, Atiku…

Shugaban Jam’iyyar APC ta Kasa, Kwamared Adams Oshiomhole ya ce ko Kotun Duniya aka je APC za ta yi wa PDP da dan takararta, Atiku Abubakar jina-jina ba Kotun Koli ba.

A ranar Laraba makon jiya  ne Kotun Zaben Shugaban Kasa ta tabbatar wa Shugaba Buhari nasarar da ya samu a zaben da aka gudanar a watan Fabrairun bana.

Bayan kammala shari’ar, Atiku ya ce hukuncin bai yi masa ba, kuma zai daukaka kara zuwa Kotun Koli.

Mista Oshiomhole ya ce yadda aka zartar da hukuncin, to yana da yakinin ko Kotun Duniya Atiku da PDP suka je, Shugaba Buhari da APC su ne da nasara.

“Saboda kotun Najeriya dai ba ta PDP ko APC ba ce. Hujjar da aka gabatar mata za ta yi amfani da shi. Wato Kotun Koli za ta sake nazarin hukuncin da Kotun Sauraren Kararrakin Zaben da kuma hujjojin da su Atiku suka gabatar, ba wani sabon abu za a sake kawowa ba,” inji shi.

Adams Oshiomole ya kara da cewar, idan aka dubi yadda alkalan Kotun Daukaka Karar suka rika kin amincewa da hujjojin da PDP da Atiku suka gabatar, to ko wanda bai san shari’a ba ya san ba su da wata madogara ta kwarai.

“Don haka su hakura su zo a hada hannu da su domin a ciyar da Najeriya gaba tare da su,” inji shi.

A cewar Oshiomole Shugaba Muhammadu Buhari a shirye yake ya sake fafatawa da Atiku a Kotun Koli. Hakazalika ita ma Jam’iyyar APC ta shirya tsaf don sake fafatawa da PDP.