✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko nasarar Tambuwal a Kotun Koli za ta dusashe APC a Sakkwato?

A kwanakin baya ne magoya bayan Jam’iyyar PDP a Jihar Sakkwato suka hadu domin tarbar Gwamna Aminu Waziri Tambuwal bayan ya samu nasara a Kotun Koli…

A kwanakin baya ne magoya bayan Jam’iyyar PDP a Jihar Sakkwato suka hadu domin tarbar Gwamna Aminu Waziri Tambuwal bayan ya samu nasara a Kotun Koli inda aka yi watsi da karar da Jam’iyyar APC ta shigar kan kalubalantar zabensa. Kwanaki kadan da wannan kuma PDP ta sake samun nasara a zaben cike-gurbi da Hukumar Zabe ta gudanar a jihar inda ta lashe dukkan kujeru hudu da aka sake zabe a kansu, kujera biyu ta ’yan Majalisar Wakilai daga kananan hukumomin Sakkwato ta Kudu da Sakkwato ta Arewa da wanda zai wakilci kananan hukumomin Isa da Sabon Birni. Biyun kuma ’yan Majalisar Dokokin Jihar ce da za su wakilci Karamar Hukumar Binji da ta Sakkwato ta Arewa ta Biyu.

Wannan nasara da PDP ta samu ya ba ta damar samun wakilai 14 a majalisar jihar inda APC take da rinjaye da ’yan majalisa 15, kuma za a gudanar da zaben cike- gurbin dan majalisar da ya rasu kwanan baya Alhaji Isah Harisu mai wakiltar Karamar Hukumar Kebbe a majalisar jihar. A Abuja kuma PDP na da Sanata daya, APC biyu, a Majalisar Wakillai tana da hudu APC na da bakwai.

A zaben Karamar Hukumar Kebbe tsakanin manyan jam’iyyun ne za a  samu wadda ta yi nasara, in PDP ta samu nasara za ta yi kankankan da APC a Majalisar Dokokin Jihar da ake ganin shugabanta yana dasawa da Gwamnan Jihar kuma ake rade-radin zai iya neman dan majalisa daya ko biyu su koma PDP tare da shi, ganin ya hau kujerar ce ba da son jam’iyarsa ba.

Zaben na Karamar Hukumar Kebbe zakaran gwajin dafi ne, kuma Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) a Jihar Sakkwato ta sanya 14 ga Maris 2020 a matsayin ranar da za a yi zaben. Hankalin Sakkwatawa ya koma kan wannan zabe da ake ganin wuri ne da magoya bayan Jam’iyyar APC suke da dimbin yawa fiye da magoya bayan PDP, idan aka lura da cewa a zaben da aka gudanar a bara ba wata kujera daya da PDP ta samu nasara a yanki duk da yana cikin kananan hukumomi biyu da Gwamna Aminu Waziri ya wakilta a lokacin yana majalisa wato kananan hukumomin Tambuwal da Kebbe. Karamar hukumar na da matukar tasiri ga jam’iyyun biyu.

A ranar da Kotun Koli ta kammala shari’ar Jihar Sakkwato aka kawo karshen dambarwar zaben 2019 a tsakanin magoya bayan Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na PDP da na magoya bayan Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, tsohon jagoran Tambuwal da ya shiga gaba a zaben 2015 har Tambuwal ya samu nasara tare da Mataimakinsa Ahmad Aliyu Sokoto.

Bayan bambancin ra’ayin siyasa da ya shiga tsakanin Tambuwal da Wamakko, Jam’iyyar APC ta tsayar da tsohon Mataimakin Tambuwal Alhaji Ahmad Aliyu don ya kalubalanci Tambuwal a wa’adinsa na biyu amma Tambuwal ya samu nasara da karamar tazara.

Lokacin da Tambuwal ya raba hanya da jagoran siysarsa Wamakko ya rungumi tsohon Gwamna Attahiru Bafarawa ya yi kokarin rashin shiga fadan ba nasa ba abin da ake ganin ya kara wa Jam’iyyar PDP karsashi har ya rike kujerarsa ba tare da Jam’iyyar APC ta mayar da shi dan kallo ba.

Sai dai jama’a da dama na ganin tunda Gwamna Tambuwal ya samu nasara a kotun bai fito da wani aikin da jama’ar jihar suke son gani ba, alhali sun sa rai su ga ya kaddamar da wasu muhimman ayyukan ci gaba da suka yi masa uzuri kasa yi a lokacin da ake shari’ar zabensa. Ana kammala shari’a sai kawai aka ji ya ci gaba da ayyukan yau da kullum na gwamnati wadanda ba zai iya rufe bakin masu adawa da jam’iyyarsa ba.

Gwamna Tambuwal ya ba da sanarwar ciyo bashin sama da Naira biliyan 65 domin aiwatar da ayyukan ci gaba a Jihar Sakkwato, idan ya samu nasarar aiwatar da ayyuka da kudin da zai karbo, tasirin Jam’iyyar APC a Sakkwato zai ragu sosai domin jiha ce da magoya bayan APC suka fi rinjaye.

Hana cin zarafin manya da kananan magoya bayan Jam’iyyar APC wani abu ne da in aka yi shi za a iya samun nasarar karya lagon APC, ganin mulki shi ne wanda yake iya tafiyar da jama’a a koyaushe sabanin adawa.

Wadansu masana a jihar suna cewa, hukuncin Kotun Koli bai rage karsashin Jam’iyyar APC ba, domin ba a ga ana canja-sheka daga APC zuwa PDP ba, abin da ake dangatawa da ko wadanda ke cikin PDP ba su samu romon dimokuradiyya ba balle wadansu su yi sha’awa su shigo a tafi tare da su.

Yanzu dai lokaci ne zai nuna inda alkiblar siyasar jihar za ta nufa a nan gaba.