✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko ya dace a biya shugabannin Majalisun Tarayya fansho har bayan rai? 4

A yayin da ake yi wa Kundin Tsarin Mulki kwaskwarima, akwai yiwuwar amincewa da dokar da za ta tabbatar da a rika biyan shugabannin Majalisun…

A yayin da ake yi wa Kundin Tsarin Mulki kwaskwarima, akwai yiwuwar amincewa da dokar da za ta tabbatar da a rika biyan shugabannin Majalisun Tarayya fansho bayan sun sauka daga mulki har zuwa mutuwarsu. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a rika biyansu irin wannan kudi? Wakilanmu sun tattauna da mabambantan mutane kuma ga ra’ayoyinsu kamar haka:

Ban amince da biyan su fansho ba – Mista Dabid Ayuba

Mista Dabid Ayuba: “Gaskiya bai dace a ce an biya shugabannin majilisun nan na kasa kudin fansho ba, domin ko shi Shugaban Majilisar Dattijai ya taba yin aikin soja kuma ana biyan sa kudin fansho; don me kuma za a ce kuma idan ya bar aikin shugabancin majilisa za a rika biyan sa fansho har na tsawon rayuwarsa? Ba a ma ce na dan wani lokaci ba, wai har na tsawon rayuwarsa; wannan ba daidai ba ne. To don Allah me wadannan mutanen za su yi da kudi ne? Kudin da ake biyansu da wanda suke samu lokacin da suke rike da wannan mukamin sun ishe su har mutuwa. Ko suna ganin su kadai ne ke son kudi ko kuma suke da bukatar wadannan kudaden? Don Allah su jingine wannan batun, domin ko muddin suka ce za su yi wa kansu wannan tsarin, to talakawa za su yi musu bore, domin haka bai dace ba ko kadan.”