✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko ya dace a biya shugabannin Majalisun Tarayya fansho har bayan rai? 6

A yayin da ake yi wa Kundin Tsarin Mulki kwaskwarima, akwai yiwuwar amincewa da dokar da za ta tabbatar da a rika biyan shugabannin Majalisun…

A yayin da ake yi wa Kundin Tsarin Mulki kwaskwarima, akwai yiwuwar amincewa da dokar da za ta tabbatar da a rika biyan shugabannin Majalisun Tarayya fansho bayan sun sauka daga mulki har zuwa mutuwarsu. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a rika biyansu irin wannan kudi? Wakilanmu sun tattauna da mabambantan mutane kuma ga ra’ayoyinsu kamar haka:

Bai dace a biya su fansho ba – Malachy Opon

Malachy Opon: “Haba, wannan rashin imani har ina? Kana ina Gwamnan Babban Bankin Najeriya wata rana ya ce kashi 25 na kasafin kudin Najeriya yana wucewa ne ga harkokin tafiyar da mulki maimakon gudanar da ayyukan ci gaban kasa; kuma ma wadannan mutanen su ce a biya su kudin fansho; alhali dokar kasa cewa ta yi ma’aikacin da ya shekara 10 yana aiki? To su a kan wace hujja ce za a biya su fansho idan sun kare aikinsu kuma ba tare da cewa ko sun kai shearun 10 ba ko a’a? Idan su ba su sani ba ne, to ’yan Najeriya na kallonsu, domin a lokacin da suke wannan aiki ba wani abu da suke saye kama daga abinci zuwa motar hawa ya kai ga masu gadinsu da kudin hasken wutar lantarki. Kai da duk wani abu da ma’aikaci ko mai karamin karfi zai biya, su dukkan wadannan abubuwan kyauta suke samunsu, bayan ’yan tafiye-tafiye nan da can, wanda ba kananan kudi suke samu ba kana ga albashi mai dan karen tsoka.