Da Dumi Dumi

Ko ya dace a rika ba kananan hukumomin kudinsu kai tsaye?

Kananan hukumomi a kasar nan sun dade da cikin halin kaka-ni-kayi, wanda hakan ta sa suke koma baya, a maimakon su ne ke kusa da al’umma kuma suke kawo abubuwan ci gaban rayuwa tun daga matakin farko. Sai dai tun bayan komawar kasar nan bisa tsarin mulkin dimokaradiyya, kananan hukumomi suka tsinci kansu cikin halin kaka-ni-kayi sabili da rashin ba su kudadensu kai tsaye daga asusun Gwamnatin Tarayya,inda gwamnonin jihohi suka mamaye komai da sunan asusun hadin gwiwa. Tun daga ranar daya ga watan nan na Yuni Gwamnatin Tarayya ta kudirin aniyar ba kananan hukumomin kudadensu kai tsaye. Wakilanmu sun jiyo ra’ayoyin jama’a a kan haka:

 

Basun zai kawo ci gaba, amma dai a yi taka-tsan-tsan – Bello Bala

Daga Muhammad Aminu Ahmad

Hakika ba kananan hukumomi kudade kai tsaye babban ci gaba ne, amma sai dai a yi ta ka tsantsan wajen yin hakan, dalili shi ne irin wadakar da ake a kananan hukumomi dole ne sai an yiwa tubkar hanci, idan ba hakan ba, za a rinka ba da kudin, amma ba zai wani amfani ga al’umma ba. Mussaman na yankunan karkara .

ADVERTISEMENT

 

Bai dace a ba su ba – Anita Jibril

Daga Jamilu Adamu

Dalili kuwa shi ne idan aka ba kananan hukumomi gashin kansu wallahi akwai matsala saboda rashin gaskiyar da yake faruwa a kananan hukumomi zai karu matuka, za ka ga shugaban karamar hukuma ya mallaki kudi na ban mamaki, haka kuma sauran manyan ma’aikatan kananan hukumomi za su azurta kansu kawai, saboda asusun hadin gwiwa nan ya nada matukar amfani koba komai Gwamnonin jihohin za su sa ido sosai domin suga an kashe kudaden kananan hukumomi ta hanyar daya dace.

 

Ai daman zalunci ne, hana kananan hukumomi kudadensu – Faruok Buba U/Danya Wudil

Daga Muhammad Aminu Ahmad

Idan ka duba a da can ai kananan hukumomi sune tushen ci gaban al’umma, tun farko an kirkiro kananan hukumomi ne, domin sune suke kusa da al’umma karkara,kuma suke aiwatar da aiyukan raya kasa domin bunkasar yankunan nasu, amma saboda da son zuciya ko in ce zalunci na wasu ‘yan tsiraru aka kassara kananan hukumomi, wai sai shugaban karamar hukuma ya zama dan amshin shata, a baka kudi, da ba zaka iya gudanar da wani aiki na ci gaban al’ummar ka ba, sai dai kawai ayi waka ci ka tashi.Gaskiya kananan hukumomi sashi daya ne daga cikin sassan gwamnati 3 Don haka ni dai ina goyon bayan a rinka bawa kananan hukumomi kudadensu kai tsaye shine alheri ga al’umma Kuma idan har kudin yana zuwa kai tsayen za kaga irin ci gaban da za a samu kuma wannan talauci da yayi yawa a kasar nan, idan har an bawa kananan hukumomin kudin nasu zai taimaka ta wajen samar da aiyuka, wanda hakan za a samu wadatuwar kudade a hannun al’umma.

 

Ya dace a ba su – Abubakar Lawal

Daga Jamilu Adamu

Dalili na kuwa shi ne idan aka baiwa kananan hukumomi gashin kansu za a samu ci gaba fiye da wanda muke samu yanzu saboda duk wata karamar hukuma za ta samu kudin aikace-aikacen ta kai tsaye ba tare da sa hannun gwamnonin jihohinsu ba, kuma game da biyan albashin ma’aikatan kananan hukumomi baza a samu tasgaroba sakamakon kudadensu yana zuwa kai tsaye.

Sauda yawa kananan hukumomi na samun matsaloli game da asusun bai daya din, saboda haka a raba su yafi dacewa.

 

Yana da kyau gwamnati ta ba kananan hukumomi kudadensu – Mujitapha Dalhatu kasuwar Kofar Wambai

Daga Muhammad Aminu Ahmad

Yana da kyau a ba su kudin, domin  shine ‘yancinsu wanda hakan zai sa talakawa su sami saukin al’amura, amma idan kudaden ba za zuwa hannun su, gaskiya, akwai matsala ko yanzu ga irin  matsalar da take faruwa babu kudi hannun mutane, wanda da ana bawa kananan hukumomi kudi, da zaka ana walwala da annashuwa a tsakanin jama’a, don haka yafi gwamnati ta samar musu kudadensu, amma ba a ce a sa kudi wai asusun hadin gwiwa, wanda bashi da wani amfani ga talaka, sai gwamna da yasu yasu, to amma idan akwai sakin mara kaga ta hannun shugaban karamar hukuma da kansila duk su ne ke kusa da talakawa kuma suke tare dasu.

 

Hakika ba su kudadensu zai bunkasa ci gaban al’umma – Muhammad Uzairu U/Danya Wudil

Daga Muhammad Aminu Ahmad

Gaskiya ni ina goyon bayan a rinka bawa kananan hukumomin kudadensu, domin hakan zai kawo kyakyawan ci gaba, kuma karamar hukuma ita ce mafi ku sa ci ga al’umma,domin nan ne inda al’umma suka san ga inda dukiyarsu take, kuma za a yi musu aiyuka kai tsaye, mussamman wajen aiwatar da aiyukan raya kasa, samar da kudade a hanun jama’a, kawo al’umma kusa da gwamnati , ga misali samar da hanyoyi na karkara, kwalbatoci, rijiyoyin burtsatse da giggina ajujuwa, da samar da tallafi ga al’umma, wanda rashin kudade a hannun kananan hukumomin duk basu da damar samar da wadannan abubuwan ci gaban rayuwar ga al’ummarsu.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya