✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko ya ya makomar matasa bayan rantsar da Buhari?

Hakika matasa sun ba da gudunmowa sosai ta fannoni da dama a lokacin da janar Buhari ke yin yakin neman zabe.Akwai misalai da dama wandanda…

Hakika matasa sun ba da gudunmowa sosai ta fannoni da dama a lokacin da janar Buhari ke yin yakin neman zabe.Akwai misalai da dama wandanda suka hada da hanyoyin sadarwa kala- kala kamar face book da makamantansu jama’a za ku iya yadda da ni saboda duk wanda yake shiga yanar gizo ya san yadda maganganu ke ta kara kaina a kan takarar janar din duk da batancin da wasu makiya ke yi wa Buharin amma matasan ba su karaya ba suna ci gaba da yada manufofinsu.

Bayan hanyar sadarwar yanar gizo ga kuma uwa uba hanyar rubuce-rubuce a cikin jaridu da kuma kungiyoyin matasan da ke amfani da kafafen yada labarai kamar wata kungiya da ake kira Muryar Talaka hakika ’ya’yan wannan kungiya sun taka rawar gani wajen Turawa da sakonnisu a kafafen yada labarai na gida da na waje musamman na waje. Saboda yadda kafafen wajen ke ba da damar bayyana ra’ayi ba tare da wani shamaki ba wannan ya kara tabbatar da samun nasarar canjin da aka dade ana bukata a wannan kasa ta mu. Bayan haka matasa hakika matasa sun fito kwansu da kwarkwata domin jefa kuri’unsu a ranar zabe musamman yadda na ga matasa sun fito a jihohi da dama musamman jihar Kano suna zagaya mazabu da dama.
Na gane wa idanuna yadda mutane suka fito, tabbas hakan ya kara tabbatar mana da cewar mutane suna bukatar canji ganin wani abin mamaki yadda matasan suka kasance a gaban akwatunan rediyoyinsu domin sauraron sakamakon. Wasu ma har da biro da takarda domin lissafa yadda sakamakon zaben yake zuwa. Tabbas wannan ya kara nuna yadda mutane musamman matasa ke nuna bukatarsu ta neman canji. Hakika ba zan yi mamaki ba ganin yadda Nijeriya ta lalace komai ya tabarbare harkar tsaro ta zama babbar matsala a kasa ga kuma yadda tattalin arziki ya zama. Hakan nema ya sa matasan da damansu ba su da aikin yi, sai ka ga matashi ya yi karatu amma abin takaici sai ka ga ya rasa aiki saboda shi ba dan wani mai fada a ji ba ne.
Komai na rayuwa ya fi karfin mutane saboda mutane sun shiga halin kaka-ni- ka yi. Wani abin takaici shine yadda matasan ke kallan yadda ’yan siyasa suke yin wadaka da kudin talakawa, wani abin takaicin ma shi ne da zarar dan siyasa ya fito neman wani mukami, babu wadanda yake nema sai matasa domin su zame masa ’yan banga, amma da zarar ya ci zabe sai ya juya wa matasan baya, daga karshe sai matasan su koma ba tsuntsu ba tarko. Tabbas ina da kyakkyawan zaton cewar wannan ya kara harzuka matasan, shi ma ya sa suka fito kwansu da kwarkwata suka kada wa Janar Buhari kuri’unsu domin samun canji.
To hakika za mu iya cewa kwalliya ta biya kudin sabulu ganin yadda aka gudanar da zabe da yadda aka tabbatar da sakamako wannan ya kara tabbatar da samun nasara.To a yanzu dai babban aikin da ke gaban sabon Shugaban kasa shi ne kalu bale da dama don haka ya zama wajibi mu taimaka masa da addu’a saboda ita ce yake bukata ta hak ane zai samu damar gudanar da alkawuran da ya dauka. Muna addu’ar Allah ya ba shi ikon gudanar da ayyuka cikin nasara.

Aminu Abdu Bakanoma
Sani mai Nagge Pro Muryar Talaka
Kano.