Da Dumi Dumi

Ko ’yan Najeriya za su ga sauyi na ci gaba a wa’adin mulkin Buhari na biyu?

Tun bayan shigarsa harkokin siyasa da takararsa ta farko ta neman shugabanci a shekarar 2003, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ke samun tagomashi da goyon baya daga miliyoyin ’yan Najeriya da suka yi amanna cewa zai iya fitar da kasar nan daga tarin matsalolin da suka yi mata dabaibayi.

Bayan yunkurinsa na hawa shugabancin kasa sau uku ba tare da nasara ba, zabbubukan da duka ya yi ikirarin cewa an yi masa murdiya, daga karshe dai Buhari ya samu nasara a shekarar 2015 a zaben da galibi aka yi amanar cewa ’yan Najeriya sun mara wa Buharin da Jam’iyarsa ta APC baya ne da zimmar cewa za a samu sabon salo na shugabanci, wanda zai kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi sassan Najeriya, musamman ta Boko Haram a Arewa maso Gabas.

Shugaban Kasa Buhari, za a iya cewa ya yi rawar gani wajen ingantuwar tsaro a shiyyar Arewa maso Gabas, duk da cewa ana samun hare-hare a wasu yankunan yankin.

Akwai bukatar kara kaimi wajen karfafa wa jami’an tsaron gwiwa, ba a shiyyar Arewa maso Gabas ba, har ma da sauran sassan da ke fuskantar matsalar tsaro. A jihohin Neja da Sakkwato har yanzu ’yan bindiga na hallaka jama’ar kauyuka wadanda ba su ji ba, ba su gani ba, duk dda yake an samu ci gaba sosai ta hanyar zama da masu kai harin.

To a daidai lokacin da Shugaba Buhari ya fara wa’adin mulki karo na biyu, kuma na karshe bisa tsarin mulki, abu ne da ya dace ya yi dubi da irin gagarumin goyon baya da kuma tsammani da ’yan Najeriya ke da shi a kansa na magance musu tarin matsaloli da ke ci musu tuwo a kwarya.

ADVERTISEMENT

Matsalar cin hanci da rashawa za a iya cewa ita ce kan gaba wajen ciyar da kasar nan baya, wacce kuma ake ganin gwamnatin Buhari za ta magance. Hukumar Yaki da Yi wa Tattalin Arziki Tu’annati  (EFCC) ta samu nasarorin karbo kudade da kadarorin gwamnati daga hannun jami’an gwamnatocin da suka gabata. To amma akwai bukatar a wannan wa’adi na mulkin na biyu Buhari ya kara kaimi wajen yaki da cin hancin da rashawa, ta hanyar tabbatar da cewa babu shafaffu da mai kamar yadda ake zargin cewa ana kawar da kai daga al’mundahana da wadansu jami’an gwamnati mai ci ke yi.

Babban abin tambaya shi ne ko a wannan wa’adin mulki na biyu Shugaban Kasar zai kawo canjin da al’umma ke fata?

Umar Ahmad Abubakar.

 

 

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya