✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko yaya shari’ar Zamfara za ta kaya a yau?

A Yau ne Kotin Koli za ta yanke hukunci a kan shari’ar da ke gabanta dangane da dakatar da dan takarar kujerar Gwamnan na jam’iyyar APC…

A Yau ne Kotin Koli za ta yanke hukunci a kan shari’ar da ke gabanta dangane da dakatar da dan takarar kujerar Gwamnan na jam’iyyar APC a Jihar Zamfara.

Kotun mai alkkalai 5 na karkashin jagorancin Babban Jojin Najeriya Ibrahim Tanko Muhammad. An ware wannan rana ne bayan sauraren dukkan sassan biyu na masu kara da wadanda ake karar, takaddamar ta biyo bayan zaben fidda dan takara a jam’iyyar ta APC ne da ya gudana a jihar a ranar 3 ga watan Oktoba 2018, inda aka tsayar da dan takara wanda na bangaren Gwamna Abdul’azeez Yari ne. Amma a karar da daya bangaren na Kabiru Marafa ya shigar, yana kalubalantar sakamakon wannan zabe na fidda dan takarar da aka yi.

A hukuncin da Babbar Kotun Jihar Zamfara ta yanke ta halatta zaben da aka gudanar na waccan rana ta 3 ga Oktoba, sai dai a karar da lauyan daya sashin ya shigar a gaban kotun daukaka kara da ke Sakkwato, su na kalubantar hukuncin da kotun ta yanke, hakazalika ita kanta uwar jam’iyyar ta kasa ta shigar da korafinta ta hannun lauyanta Damian Dodo (SAN), inda take bukatar babbar kotun ta yi watsi da hukuncin da kotun daukaka karar ta yanke, ta bi hukuncin da babbar kotun Jihar Zamfara ta yanke, a kan takarar da jam’iyyar ta gabatar. Sai dai lauyan sashin Kabiru Marafa, Mike Ozekhome (SAN) ya nemi kotun ta yi watsi da daukaka karar da sashin Gwamna Yari suka yi, domin bai cancanta ba kuma kama ta ya yi su bi tsarin kotun daukaka kara amma ba kotun koli ba. Haka kuma Ozekhome ya kuma bukaci kotun, bayan ta yi watsi da lamari, ta ma bukaci su biya wata tara.

Bangaren Gwamna Yari da jam’iyyar APC sun gabatar da koken su a kan hukuncin da kotun daukaka kara ta Sakkwato ta yanke na yin watsi da hukuncin da babbar kotun zamfara ta yanke akan sahihancin zaben fidda dan takarar da akayi, a waccan rana, domin akwai hujjoji da ke nuni da cewa ba a gudanar da zaben bisa tsarin kai’dojin hukumar zabe mai zaman kanta ba, da kuma tsarin mulkin jam’iyyar. Wannan hukunci ya shafi duk ‘yan takarar jam’iyyar APC a jihar ta zamfara a babban zaben da ya gudana.

Saboda wannan matsala a Jihar Zamfara na rushe dukkan ‘yan takarar jami’yar APC a zaben kasa, tasa Kotun Koli ta ware ranar 16 ga watan mayu, domin sauraren  koken da aka shigar a kan dakatar da ‘yan takarar jami’yar. Sai dai kotun kolin tace ta gano kura kurai da yawa a karar da aka shigar da tayi sanadiyar dakatar da ‘yan takarar jami’yar APC. Tun a ranar 2 ga watan mayu kotun kolin ta dage zama sauraren shari’ar, zuwa ranar 16 ga watan, domin bawa dukkan sassan damar yin nazari akan kura kuren da ke kunshi cikin tsarin.

Dagewar kuma ya biyo, bayan lauyan sashin Kabiru Marafa, Mike Ozekhome ya gabatar ne, inda ya nemi kotun data bada dama akan ya sake yin nazari akan dukkan sauran takardun da aka gabatar akan lamarin. Sai dai lauyan sashin Gwamna Abdul’azeez Yari, Lateef Fagbemi (SAN) ya kalubanci yin hakan, kana ya shaidawa kotun cewar akwai hujjoji da bayanai na dukkan sassan akan lamarin, da suka hada da dukkan bayanai. Jin koken na zuwa ne mako biyu kacal da ranar mika mulki ta 29 ga watan mayu, wanda wannan lamari ya jawo batutuwa da dama a tsakanin alumma, da kuma barin jami’yar APC babu dan takara a mukamai na zabe a jihar ta zamfara, daga cikin mukaman da wannan lamari kan iya shafa sun hada da Mukamin zababben Gwaman jihar Muktar Shehu Idris, Sanata Abdul’azeez Yari mai wakiltar Zamfara ta Yamma sai Aliyu Ikra Bilbis Zamfara ta tsakiya da Kaura Tijjani Yahaya Zamfara ta Arewa, da kuma ‘yan majalisar wakilai ta tarayya guda 7 dana majalisar jihar su 24 wadanda duk sun fito daga bangaren Gwamna Yari, ba daya bangaren ba.

Duk da cewar  jam’iyar PDP itace tazo na biyu a yawan kuri’un da aka kada a zaben, ga misali a zaben Gwamna  Idris ya samu kuri’u 534,541 sai ma bi masa Dr Bello Muhammad na jami’yar PDP ya samu kuri’u 189,452,

Bangaren Gwamna Yari na APC shine ya shigar da karar gaban kotun koli inda yake kalubantar hukuncin da kotun daukaka kara a sokoto ta yanke, na ajiye hukuncin da babbar kotu zamfara ta yanke na halasta zaben fidda ‘yan takara da aka yi a ranakun 3 da 7 na watan oktoba 2018.

Da yake gbatar da hukunci akan  daukaka karar da bangaren Marafa ya shigar wadda mai shari’a Tom Yakubu ya jagoranta, cewa yayi waccan karamar kotun ta kasa, duba lamarin a tsanaki akan zaben fidda ‘yan takarar na APC da akayi. Inda kotun tace bangaren Yari sun sabawa tsarin hukumar zabe mai zaman kanta, wajen gudanar da zaben fidda ‘yan takarar, domin haka ta rushe wananan zabe da duk ‘yan takarar da aka tsayar.

Sai dai kafin wannan umarni na karshe, wata kotun daukaka kara a Abuja a ranar 21 ga fabreru a sake yin duba da tayi akan koken da bangaren Yari  ya shigar, ta rushen hukincin da aka zartar na ranar 25 ga watan janairu, a babbar kotun Abuja, wanda ya dakatar da kudirin hukumr zabe mai zaman kanta na kin amincewa da dukkan ‘yan takarar APC a jihar zamfara.

Sai da Manyan Lauyoyi sun tofa albarkacin bakinsu akan wannan lamari da kuma ikon kotun koli na yanke hukunci akan halin da jami’yar APC take ciki a jihar ta zamfara, kafin nan da ranar 29 ga wata mayu na mika mulki da kuma ranar 6 ga watan yuni inda za a kaddamar da ‘yan majalisu na tarayya a majalisa ta 9.

Babban Lauya Owonikoko (SAN) cewa ya yi tun da za a yanke hukunci a yau, ai ba za su yi saurin baki ba na cewa jihar za ta iya kasancewa dukkan mukaman su zama gurbi, ko a’a. Shi kuma Mike Ozekhome (SAN) wanda lauya ne a cikin lamarin cewa ya yi yana da yakinin za a kammala komai kafin ranar mika mulki, domin ta iya yiwuwa bangarorin su janye wasu daga cikin kudirorin da aka gabatar a gaban kotun, wanda hakan zai ba kotun kolin saukin yanke hukunci a kan lamarin. Shi ma Ahmed Raji (SAN) cewa ya yi kotun za ta yanke hukuncin cikin kankanin lokaci.