✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko yunkurin ceto Tafkin Chadi zai haifar da da mai ido ga harkar noma?

Tafkin Chadi ya kasance wata cibiya ta samar da ruwa da abinci ga miliyoyin mutane a Afirka ta Yamma, amma yanzu ya kafe da kimanin…

Tafkin Chadi ya kasance wata cibiya ta samar da ruwa da abinci ga miliyoyin mutane a Afirka ta Yamma, amma yanzu ya kafe da kimanin kashi tara cikin goma saboda sauyin yanayi da karuwar jama’a da kuma yawan noman rani da ake yi a kusa da shi.

A wani bincike da Gidan Rediyon BBC ya yi, ya bayyana cewa “Tun a 1980 aka fara yunkurin ceto tafkin domin hana shi kafewa. Masana da yawa sun nuna shakku game da yunkurin a matsayin wanda ba mai tasiri ba, kuma zancen kawai, musamman da suka ji cewa za a janyo ruwa daga Kogin Kongo wanda ke da nisan kilomita  2,400 zuwa Tafkin Chadi don sake cika shi da ruwa domin ya dawo kamar yadda yake a baya.

’Yan Najeriya da ke nuna shakku kan wannan aiki, saboda ganin cewa gwamnatocin da suka gabata sun kasa aiwatar da aikin, sun ce da alama ’yan siyasar da ke yin wannan yunkuri romon-baka kawai suke yi. Sai dai ministoci da injiniyoyi, wadanda suka yi taro a Abuja kwanakin baya kan yadda za a hana Tafkin Chadi kafewa, sun ce za su tabbatar burinsu na hana kafewar tafkin ya cika.

Tafkin Chadi ya samu koma-baya da kimanin kashi 90 cikin 100 tun daga shekarun 1960 saboda sauyin yanayi da karuwar jama’a da aikin noman rani da ba a tsara shi ba. kasashen Najeriya da Nijar da Chadi da Kamaru ne suka fi cin moriyar tafkin, domin kuwa yana sanar wa kimanin mutum miliyan 20 zuwa 30 ruwan da suke amfani da shi.

Amma duk shekara zaizayewar kasa na ci gaba da yin illa ga yankunan, lamarin da ya jefa mutanen da ke sana’o’i irin su kamun kifi da noma da kiwo a yankunan cikin garari. Majalisar dinkin Duniya ta ce mutum miliyan 10 da dubu 700 da ke zaune a yankin Tafkin Chadi na bukatar agaji domin su ci gaba da gudanar da rayuwa yadda ya kamata. “A baya mukan wuce gonakin masara a kan hanyarmu ta zuwa tafkin kuma akwai jiragen kwale-kwale da ke kai-komo a cikinsa, inda ake samun masunta da ke cin kasuwar kifi, inji Malam Bale Bura, wanda ya girma a yankin a shekarun 1970 kuma yanzu yana aiki da kungiyar masunta ta yankin Tafkin Chadi.

Yanzu manoman da ke amfani da tafkin ba su da yawa. Wannan ne dalilin da ya sa wakilan da suka yi taro a Abuja suka yanke shawarar sake waiwayar batun ceto tafkin wanda wani kamfanin injiniyoyin Italiya Bonifica Spa ya soma a 1982.

An kaddamar da wani shiri mai suna Transakua – wanda zai sa a gina magudanar ruwa mai tsawon kilomita 2,400 da za ta taso daga babban Kogin Kongo ta ratso ta yankin Chadi da ke bakin kogi, sannan ta gangaro cikin Tafkin Chadi. 

Shirin ya ba da shawarar cewa a duk shekara a kai ruwa mai yawan mita biliyan 100 zuwa ga madatsun ruwa daban-daban na yankin domin samar da hasken wutar lantarki. “Na tura daya daga cikin injiniyoyinmu Amurka ya sayo taswirar Afirka ta hakika, wadda sojin saman Amurka suka tsara, wacce ke dauke da bayanai kan lungu da sakon tafkin,” inji Marcello bichi, wani injiniyan kasar Italiya wanda aka dora wa alhakin gudanar da aikin a farkon shekarar 1980.

“Bayan mun kwashe watanni muna nazari a kai mu kadai, na shaida wa masu ruwa-da-tsaki kan batun, cewa za mu iya ceto tafkin daga kafewa,” inji shi. An mika kwafe 500 na tsare-tsare kan yadda za a ceto fafkin daga kafewa ga wakilan gwamnatocin Afirka da hukomomin kudi na duniya a 1985.  

Ya kara da cewa “Amma babu wanda ya dauki mataki.” Shekara fiye da 30 bayan hakan, an soma mayar da hankali kan batun, bayan da aka fahimci cewa rikicin da ke faruwa a yankin musamman na kungiyoyin tayar da kayar baya, yana da alaka da kafewar tafkin da kuma kaurar da ake yi daga gare shi. A shekarar 2014, na hau motar bas inda na je birnin Maiduguri domin zuwa Tafkin Chadi. Akwai motoci masu sulke a gaba da bayana, kuma a gefena na dama wani sojan Najeriya ne a kwance yana kwasar barci.

Mun je Kirenawa, daya daga cikin kauyukan da mayakan Boko Haram suka addaba. A lokacin da muke tafiya, mun yi karo da yankuna da dama da aka yi watsi da su, inda kuma ga ayyukan ci gaba da dama da gwamnati ta yi watsi da su. An kona gidaje sannan aka bar mutane cikin halin kaka-na-ka-yi, inda a gaban idanunsu ake kashe ’yan uwansu. A duk kauyen da muka je, jama’a na korafin cewa matasa ba su da aikin yi kuma ba su da makoma tagari.

Wannan halin da matasa ke ciki ne ya bai wa shugabannin Boko Haram damar daukarsu aiki a matsayin mayakan kungiyar. An rika ba su kudi kadan da yi musu alkawarin samun horo, sannan a ba su bindiga lamarin da ya sa da dama daga cikinsu suka shiga kungiyar.

Tabbas ba kafewar da Tafkin Chadi ke yi ne kadai abin da ke haddasa hare-haren masu tayar da kaya ba – abubuwa da dama da suka hada da rashin gudanar da mulki nagari sun taka muhimmiyar rawa, amma dai talauci shi ne jigon wadannan matsaloli. Na san matasa da dama a kauyenmu da suka rungumi harkar tayar da kayar baya,” inji Malam Bura.

A lokacin da wakilai suka taru a Abuja domin tattaunawa kan yadda za a fuskanci matsalar kafewar Tafkin Chadi ne aka sace ’yan makarantar mata ta Dapchi sama da 100. A wurin taron, an amince kamfanonin Bonifica da Power China, kamfanin da ya gina madatsan ruwan The Three Gorges Dam daga Kogin Yangtze, su gudanar da bincike kan yadda za a tunkari matsalar. Sun bayyana cewa za a kashe kusan Dala biliyan 50 idan ana so Gidauniyar ceto Tafkin Chadi ta soma aiki.