Mataimakin Ministan Harkokin wajen Siriya, ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta mika wuya ba, kan barazanar harin taron dangin Amurka da kawayenta, ko da za a yi yakin duniya na uku.
Mista Faisal Mukdad ya ce gwamnatinsu za ta dauki “kowane irin mataki,” don kare kanta daga shirin cutar da Gwamnatin Bashar al-Assad, kan zargin amfani da makamai masu guba a kan fareren hular kasar.
Shi kuwa Shugaban Amurka Barack Obama ya bayyana cewa ba za a yarda da gaskiyar kasashen duniya ba, idan har ba a mayar da martani a kan harin da aka kai wa fararen hula da makami mai guba a Siriya ba.
Shugaba Obama yana neman amincewar majalisar kasarsa da goyon bayan manyan kasashen duniya, don daukar matakin soja a kan Gwamnatin Shugaban Siriya, Bashar al-Assad.
Ya kuma tabbatar da cewa daukar matakin soja a kan gwamnatin ba zai warware matsalar ba, amma dai akwai bukatar a yi hakan don yin gargadi.
Ko za a yi yakin duniya na uku Siriya ba za ta mika wuya ba – Mataimakin Minista
Mataimakin Ministan Harkokin wajen Siriya, ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta mika wuya ba, kan barazanar harin taron dangin Amurka da kawayenta, ko da…