✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko zan mutu sai na sayar da Kamfanin NNPC in aka zabe ni – Atiku

Dan takarar Shugaban Kasa a karkashin Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana Kamfanin Man Fetur ta Kasa (NNPC) da cibiyar ’yan Mafiya inda ya…

Dan takarar Shugaban Kasa a karkashin Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana Kamfanin Man Fetur ta Kasa (NNPC) da cibiyar ’yan Mafiya inda ya yi alkawarin zai sayar da kamfanin. Da yake magana a Legas wajen ganawa da ’yan kasuwa, Atiku ya kuma soki kasafin kudin bana da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya mika wa Majalisar Dokoki ta Kasa. Atiku ya ce ya taba ba tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo wanda ya kasance masa Mataimakin Shugaban Kasa shawarar a sayar da Kamfanin NNPC amma ya ki amincewa da haka. Ya ce abubuwan da Kamfanin NNPC zai rika samarwa  zai bunkasa sosai idan aka sayar da shi, inda ya ce ko zai mutu zai sayar da kamfanin.

“Na shirya da gaske don sayar da NNPC koda za su kashe ni sai na yi haka. Lokacin da muka samu mulki na je ofishin shugabana na ce, ‘Yallabai akwai cibiyoyin mafiya biyu a gwamnati. Daya daga ciki shi ne Kamfanin NNPC, yayin da dayan shi ne Hukumar Wutar Lantarki ta Kasa (NEPA). Na ce, matukar ba mu kawar da wadannan cibiyoyin mafiyoyi ba ba za mu ci gaba ba. Kawai mu sayar da su kawai… a takaice dai da gaske nake yi wajen sayar da dukiyar gwamnati ga ’yan kasuwa,” inji shi.

Kuma ya sha alwashin inganta tsarin yin kasafin kudi idan aka zabe shi tare da kai kasar nan matakin kudi na Dala tiriliyan daya. Ya ce, masu zuba jari da dama sun rasa biliyoyin Naira saboda rashin ingancin tsarin tattalin arziki na wannan gwamnati, inda ya ce shirin Farfadowa da Bunkasa Tattalin Arziki (ERGP) na gwamnatin Buhari ba zai iya magance matsalolin tattalin arziki ba.

Atiku ya ce, “Muna bukatar wani kasafin kudi na jama’a da zai fi bayar da fiffiko da mayar da hankali a kan tagwayen matsalolin rashin aikin yi da talauci.”

Ya ce, “Karuwar rashin aikin yi da talauci a Najeriya suna damalmala tsarin tattalin arziki sosai kuma suna jawo a rasa dama mai yawa ga muhimman hanyoyin bunkasa,” wadanda ya ce “Suna jawo muguwar barazana ga harkokin rayuwa,” inji shi.