Da Dumi Dumi

Kocin Arsenal na murmurewa daga cutar Kurona

Dan kwallon kulob din Arsenal Lucas Torreira ya  ce kocinsu Mikel Arteta wanda ya kamu da cutar Kurona ya sanar da su ta waya cewa yana samun sauki.

Mikel Arteta shi ne na farkon wanda ya kamu da cutar a Ingila a bangaren masu horar da kwallon kafa a ranar Alhamis da ta wuce. Bayan ya kamu da cutar ce sai aka killace ’yan kwallon kulob din Arsenal inda daga bisani  mahukunta suka dage gasar Firimiyar Ingila zuwa 4 ga Afrilu.

Daga baya ne aka samu rahotannin da suka nuna wadansu daga cikin ’yan kwallon Eberton da Leicester City ma sun kamu da cutar.

Idan za a tuna a ranar Juma’ar da ta gabata ce Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila ta dage gasar Firimiya zuwa 4 ga Afrilu saboda yaduwar cutar Kurona.

ADVERTISEMENT
Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya