✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Kocin Libya ya ajiye aiki

Rahotanni da ke fitowa daga Libiya sun tabbatar da cewa kocin Libya, Adel Amrouche ya ajiye mukaminsa kwanaki kadan kafin kasar ta kece raini da…

Rahotanni da ke fitowa daga Libiya sun tabbatar da cewa kocin Libya, Adel Amrouche ya ajiye mukaminsa kwanaki kadan kafin kasar ta kece raini da Najeriya.

A ranar Talatar da ta gabata ce kocin ya bayar da sanarwar ajiye mukaminsa, inda wani rahoto ya ce tuni kocin ya koma kasarsa ta ainihi Tunisiya.

Rahoton da kafar watsa labarai ta Naij.com ta ce kocin ya samu sabani ne  da Hukumar Kwallon Kafa ta Libya bayan an kwashe wata shida ba tare da an biya shi albashi ba. Wannan da wasu dalilai suka sanya kocin ajiye aiki nan take ba tare da bata lokaci ba.

Rahoton ya kara da cewa tuni hukumar kwallon kafar ta amince Mataimakin Kocin Omar Al-Miryami a matsayin wanda zai jagoranci Libya a fafatawar da za su yi da Najeriya.

Masana harkar kwallo suna ganin wannan ajiye aiki da kocin ya yi zai iya shafar kwazon da ’yan kwallon Libya ke nunawa, musamman ganin kawo yanzu kasar ce take saman teburi a Rukunin E da maki 4.

Sai dai magoya bayan kungiyar Super Eagles sun gargadi ’yan wasan Najeriya da kada su kuskura su raina kasar Libiya, in ba haka ba za su sha mamaki.