✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kofin Afirka: ‘Yan wasan Kano Pillars sun fara gwajin COVID-19

A shirye-shiryenta na fara buga wasan cin Kofin Kalubale na nahiyar Afrika a kasar Senegal, kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta fara yi wa…

A shirye-shiryenta na fara buga wasan cin Kofin Kalubale na nahiyar Afrika a kasar Senegal, kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta fara yi wa ’yan wasa da jami’anta gwajin COVID-19.

Jami’in Hulda da Jama’a na Kano Pillars, Rilwanu Idris Malikawa Garu, ya ce duk dan wasa da wakilin kungiyar da zai je gasar wajibi ne a yi masa gwajin na COVID-19.

“Mun fara yin gwajin ne domin a cika ka’idoji da sharuddan da Hukumar Yaki da Yaduwar cututtuka ta Kasa (NCDC), Hukumar Kwallon Kafa ta Kasa (NFF), da Hukumar Kwallon Kafa ta nahiyar Afrika (CAF) suka gindaya”, inji shi.

Ana sa ran Kano Pillars za ta kara da kungiyar Jaraaf ta kasar Senegal a zagayen farko na gasar da za a buga ranar 28 ga watan Nuwamba a Senegal.

Za kuma a buga zagaye na biyu a Najeriya sati biyu bayan kammala zagayen farko a kasar Senegal.

Kungiyar ta Kano Pillars ta kammala dukkan shirye-shiryen tafiya zuwa Senegal don buga wasan na zagayen na farko a can.