✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kofin AITEO:  Ganduje ya yi wa Kano Pillars ruwan Dala

A ranar Litinin da ta gabata ce Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ya saka wa ’yan kwallon Kano Pillars da jami’ansu inda ya…

A ranar Litinin da ta gabata ce Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ya saka wa ’yan kwallon Kano Pillars da jami’ansu inda ya ba kowanensu kyautar Dala dubu 1 (kimanin Naira dubu 362).

Gwamna Ganduje ya saka wa ’yan kwallon da jami’ansu ne jim kadan bayan sun sauka a Kano daga Jihar Kaduna inda suka samu horo bayan da suka lashe Kofin Kalubale na kasa da aka fi sani da AITEO.

Idan za a tuna Kano Pillars ta doke Neja Tonrnadoes a wasan karshe a garin Kaduna a bugun finareti da ci 5-4 wanda hakan ya sa ta dauki kofin bayan shekara 66.

A yayin liyafar cin abinci da Gwamnan ya shirya wa ’yan kwallon da jami’ansu, ya jinjina musu game da wannan namijin kokari da suka yi wajen lashe wannan kofi a karon farko bayan shekara 66.

Gwamnan ya ce lashe kofin da suka yi ya daukaka martabar jihar da Arewacin kasar nan a idon duniya inda ya hore su da su ci gaba da nuna kwazo don ganin sun samu nasara a gasar cin Kofin Kalubale na Nahiyar Afirka da za su fafata a kwanan nan.

“Zan ci gaba da saka muku da alheri idan kuka ci gaba da nuna kwazo wajen daukaka martabar jihar nan.  Wannan kyauta da na yi muku tukuici ne kawai don bai isa a ce na saka muku 100 bisa 100  game da farin cikin da kuka sanya daukacin magoya bayan Pillars da al’ummar Jihar Kano a ciki ba,” inji Ganduje.

A bangaren jami’ai da ’yan wasan sun jinjina wa Gwamnan game da karramawar da ya yi musu, inda suka sha alwashin ci gaba da nuna kwazo don daukaka martabar Pillars a wasannin da za su yi nan gaba, musamman a gasar cin kofin kalubale na Afirka.