Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Kofin AITEO:  Yadda Pillars ta zama zakara bayan shekara 66

A ranar Lahadi 28 ga Yulin da ya gabata ne kulob din kwallon kafa na Kano Pillars da ake wa lakabi da (Sai Masu Gida) ya samu nasarar lashe Kofin Kalubale (AITEO Cup) a karon farko cikin shekara 66. Rabon Kano da lashe wannan kofi  tun 1953.

A bara kulob din ya kusa daga kofin bayan ya kai wasan karshe inda suka fafata da kungiyar kwallon kafa ta Enugu Rangers a filin wasa na marigayi Stephen Keshi da ke Asaba na Jihar Delta.

ADVERTISEMENT

Sai dai a wancan lokaci, Pillars ce take kan gaba har zuwa minti na 50 bayan ta zura kwallaye uku a ragar Rangers amma abin mamaki da takaici kafin a tashi wasan sai da Rangers ta farke kwallaye ukun da hakan ya sa aka yi bugun finareti kuma aka doke Pillars.

Wancan al’amari bai yi wa gwamnatin Kano da magoya bayan kulob din dadi ba, amma haka suka rungumi kaddara.

ADVERTISEMENT

A bana da yake kulob din yana da sa’a sai  ya sake zuwa wasan karshe inda ya fafata da kulob din Niger Tornadoes da ke Minna a filin wasa na Ahmadu Bello da ke Kaduna.

Dubban jama’a ne suka kalli wasan karshen ciki har da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano da Mataimkinsa Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna da kuma Gwamnan Jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello da sauran manyan baki.

Wasan ya kayatar sosai domin dukkan kungiyoyin biyu sun nuna kwarewa da bajinta, inda suka rika kai wa juna hari.  Sai dai har aka tashi wasan babu kungiyar da ta jefa kwallo a ragar ’yar uwarta. Hakan ya sa aka yi bugun finareti, inda Pillars ta zura kwallaye hudu a raga yayin da Niger Tornadoes ta zura kwallaye uku aka tashi Pillars ta yi nasarar lashe kofin da ci 4-3.

Jim kadan bayan an tashi wasan sai filin ya rude da murna daga ’yan kallo musamman magoya bayan Kano Pillars don nuna murnarsu game da lashe wannan kofi a karon farko cikin shekara 66.

Daga cikin mawakan da suka taya Pillars murna a filin wasan har da Rarara da ayarinsa.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya nuna farin cikinsa lokacin da ya aika sakon taya murna ga kungiyar. “Ina farin ciki game da wannan nasarar da kuka samu na lashe Kofin Kalubale (Aiteo Cup) bayan shekara 66.  Al’ummar Jihar Kano baki daya suna jinjina muku. Sannan ina yaba wa shugabanni da ’yan wasa da kuma daukacin magoya bayan Kano Pillars game da wannan nasara da kuka samu.  Ko shakka babu gwamnati za ta saka wa ’yan kwallon da zarar sun koma Kano daga sansanin da suke samun horo a Kaduna don fuskantar wasannin da ke gaba,” inji shi.

Gwamna Abdullahi Ganduje ya umarci kulob din Pillars ya ci gaba da zama a garin Kaduna don samun horo don fuskantar gasar cin Kofin Kalubale na Afirka da za a yi nan gaba kadan, inda Pillars za ta wakilci kasar nan.

Ana sa ran a ranar Litinin mai zuwa ne Kano Pillars za ta koma Kano bayan ta gama samun horo a Kaduna inda Gwamna Ganduje ya ce zai shirya musu liyafar cin abinci da kuma ba su kyaututtuka.

Tun bayan da aka mayar da sunan kofin zuwa Aiteo Cup a shekarar 2017 babu wani kulob da ya taba lashe kofin daga Arewa sai Kano Pillars.

A shekarar 2010 ce Kaduna United ta taba lashe kofin amma a lokacin ana yi masa lakabi ne da Kofin Kalubale na Koka-Kola  (Coca-Cola FA Cup).

An fara gasar cin wannan kofi ne tun a 1942 amma sai a 1953 Kano ta dauki kofin a na farko sai kuma a bana da ta sake daukar na biyu a tarihi.

Kano Pillars dai ta samu kyautar Naira miliyan 25 ne daga Hukumar NFF saboda lashe wannan kofi.