Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Kofin FA na Ingila: Arsenal za ta hadu da Man United

A ranar Litinin da ta wuce ce Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila (FA) ta fitar da jadawalin gasar cin Kofin Kalubale na Ingila (FA) zagaye na hudu.

A jadawalin, wasan da ya fi daukar hankali shi ne wanda kulob din Arsenal zai hadu da na Manchester United.

ADVERTISEMENT

Arsenal ce ta fi yawan daukar wannan kofi, inda ta dauka har sau 13 yayin da Manchester United ke biye da ita da dauka 12.  Don haka ana ganin wasan zai yi zafi saboda dukan kungiyoyin biyu za su yi kokarin kare martabarsu ce don ganin sun sake lashe wannan kofi a wancan lokaci.

Kulob din Manchester City kuma zai hadu da na Burnley yayin da kulob din Crystal Palace zai hadu da na Tottenham.

ADVERTISEMENT

Kungiyoyi 32 ne suka kai wannan mataki na zagaye na hudu.

Ana sa ran dukan wadannan wasanni za a yi su ne a tsakanin ranakun 25 zuwa 28 ga Janairu, 2019.