✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kofin Kalubale: Kano Pillars ta ga samu, ta ga rashi

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta ga samu ta kuma ga rashi a shekaranjiya Laraba, bayan kulob din Enugu Rangers ya doke ta da…

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta ga samu ta kuma ga rashi a shekaranjiya Laraba, bayan kulob din Enugu Rangers ya doke ta da ci 4-2 a bugun fanariti a wasan karshe na cin Kofin Kalubale da ake kira Aiteo Cup na bana.

Wasan wanda ya gudana a Jihar Delta, ya samu halartar kimanin ’yan kallo dubu 22.

Minti biyar da fara wasan Rabi’u Ali na Kano Pillars ya zura kwallon farko a raga, kafin Alhassan Ibrahim ya zura kwallo ta biyu inda aka tafi hutun rabin lokaci a haka.

Bayan an dawo daga hutun  ne  sai  Nymar Awagua ya zura kwallo ta uku a ragar Enugu Rangers ya zamo Kano Pillars tana da ci 3-0.

Kowa ya zaci Pillars ta riga ta lashe kofin amma a daidai minti na 77 sai dan kwallon Enugu Ranges Itoya ya jefa kwallo a ragar Pillars, kuma a minti na 82 Chidera Ezeh ya zura kwallo ta biyu, sai Ibrahim Ajani ya fanshe wa Enugu Rangers a daidai minti na 91.

Hakan ya sa aka yi bugun fanariti inda Enugu Rangers ta samu nasara da ci 4-2.

Magoya bayan Kano Pillars sun yi bakin ciki game da wannan sakamako ganin kulob din ya barar da damar da ya samu ta lashe wannan kofi a karon farko a tarihi, amma bai yi haka ba.