Rahoton da kafar watsa labarai ta Naij.com ta kalato ya nuna kulob din Liberpool ne ya fi kowane kulob a Ingila yawan lashe kofuna.
Bayan kulob din ya samu nasarar lallasa Chelsea a Kofin Super Cup a shekaranjiya Laraba, yanzu kulob din yana da kofuna 43 a tarihi inda ya doke na Manchester United da ke da kofuna 42.
A wasan da Liberpool ta yi da Chelsea a shekaranjiya Laraba, an tashi ne da ci 2-2 inda aka yi bugun finareti kuma Liberpool ce ta samu nasara da ci 5-4.
Sakamakon wasan bai yi wa magoya bayan Chelsea dadi ba, ganin yadda a makon jiya kulob din United ya lallasa Chelsea da ci 4-0 a gasar Firimiya ta Ingila.
Masana harkar kwallo suna ganin sabon Kocin Chelsea Frank Lampard yana fuskantar kalubale ganin yadda kulob din ya fara kaka ta bana da kafar hagu.