Da Dumi Dumi

korafe-korafe da ake yi a kaina ba su damuna – Al-Mustapha

Ranar Lahadin da ta gabata ce Manjo Hamza Al-Mustapha ya ziyarci gidan Sardaunan Matasa, Mohammad ibrahim Gashash a Kaduna inda ya gana da manema labarai ciki har da Aminiya a kan yadda za a samar da zaman lafiya a kasa baki daya:Manjo Hamza Al-Mustapha

Aminiya: Bayan fitowa daga tsare ka da aka yi kake zagaye-zagaye kana jawabai a kan yadda za a samu zaman lafiya. Ko za ka fada mana dalilanka na daukar wannan salo?
Al-Mustapha: Da farko babu abin da zai dauwama in babu zaman lafiya. Na biyu ba na fito ne a kan kaina na shiga wadannan kiraye-kiraye ba. Akwai wadanda suka same ni suka yi min maganganu da dama da dama ina da alaka da su a kan taimaka wa matasa. Na san su kuma muna aiki tare da sun tun da dadewa. Kuma irin bayanan da ake samu daga bangarorin Arewa ba su da dadin ji, suna da tsoratarwa sosai. Saboda haka wanda ya san ma’anar zaman lafiya zai ga cewa yana da mahimmanci ya ba da gudunmawarsa wajen ganin an samu zaman lafiya da hada kai a bar wadannan bambance -bambance kuma a kawar da mutane masu saka kulle-kulle a zukatan mutane suna haddasa fitina a tsakaninsu. Babu kasar da za ta dauki tashin hankali a matsayin hanyar da ta dace.
Aminiya: Me kake ganin ya kawo aka samu sabanin wanda kila kafin a tsare ka babu irin wannan bambanci kamar yadda yake a yanzu?
Al-Mustapha: Wannan akwai sakaci fisabilillahi a wurin masu mulki. Duk inda ka ga wanda ke da mulki yana saka bambance bambance a cikin mutane domin ya samu abin da yake so, to shi irin wannan mai mulki abin da mutane ya kamata su yi shi ne su nuna masa gaskiya a kan ya gyara. Na biyu kuma a yi masa ko a yi musu addu’a. Kuma ya danganta da yadda ake ganin mutanen amma rashin gaya wa wanda ke mulki gaskiya hadari ne. Kuma na yi imanin cewa wadanda suke kan mulki idan suka so kansu baraka za ta shiga kuma bambance bambance za su shiga a tsakanin al’umma. Hadari ne ga su masu mulkin, hadari ne ga su jama’a. Abin da ya faru a baya wannan ya isa na karanta abubuwa da dama tunda na fito wasu abubuwan bai ma kamata su faru ba. Ai mun tashi mun ga iyayenmu da kakannninmu yadda suka zauna lafiya. Me ya sa yau ta zama daban da jiya? Ke nan ya nuna akwai sakacin wadansu mutane da ba za mu yarda da hakan ba. Idan kashe-kashen da suka faru a jiya an dauke su ba wani abu ba ne, to kai ka san abinda zai faru gobe ba zai yi kyau ba. Duk dan Adam na da hakki a kan taimaka wa kasarsa ta yadda za a zauna lafiya. Idan ka duba mulkin kansa dalilan samunsa shi ne a zauna lafiya.Yawancin wadanda ke amfani da abubuwan da ke faruwa a wajen mutanen mu na haddasa fitina ba za su taba fita daga kan iyakar kasar nan ba su je wata kasa su aikata hakan su zauna lafiya ba. Sun san doka za ta yi aikinta.
Aminiya: Akwai mutanen da suka nada wa wannan yunkuri naka rawani na siyasa. Ka taba jin wannan labari kuma mene ne gaskiyar wannan tafiya?
Al-Mustapha: Na sha jin haka domin akwai mutanen da ba sa son yin hakan saboda ta haka suke samun abin da suke sawa a aljihunsu. Za su iya kiransa da kowane suna, ni ba na son fitina tun fil azal kuma yana daga cikin dalilan da ya sa na shiga soja. Ba na shiga soja domin abin duniya ne ba, kishin kasata ya ni a soja. In da abin duniya nake so ba zan shiga soja ba, domin gidanmu gidan kasuwanci ne. Manyan da ke cikin gwamnati sun tashi ana renonsu su a gidanmu. Saboda haka inda maganar neman kudi ce da ban shiga soja ba.
Aminiya: Mene ne gaskiyar cewa har yanzu ba ka ajiye kakin soja ba?
Al-Mustapha: Eh, to akwai dokoki da ake bi ga duk wanda ya samu kansa a irin yadda na samu, ba ma irin nawa yake ba wanda abu sne abo a cikin dokar soja. Saboda haka sai hukumar sojoji ta zauna sannan su tantance abubuwan da ya faru da ni. Wani su gyara wani kuma a bi ka’idoji na doka, a nan muke yanzu.
Aminiya: Ina gaskiyar cewa wai an kara maka girma?
Al-Mustapha: Sai a bari sai hukumar soja ta gama zamanta tukuna. Mutane ne saboda sanin yadda hakkinmu yake shi ya sa suke ganin babu wata-wata sai dai a yi hakan. Ni ba na sauri kuma koda kurtu nake abin da ya dame ni shi ne ina tsaya a kan kafafuna da sunan dan kasa nagari, idan haka ya faru alhamdulillahi.
Aminiya: Bayan taron matasa a nan Kaduna wasu sun yi zargin cewa kana taka rawar ne da bazar wasu, kamar Shugaban kasa Jonathan. Me za ka ce game da wannan zargi?
Al-Mustapha: Duk na ji irin wadannan zance na mutane, amma abin da na yi shi tun a 1984 har zuwa lokacin da aka kama ni a 1998 yau don na fito na ci gaba da shi sai a fassara shi da wani suna na daban. A 1984 ai Janar Buhari ke mulki har zuwa lokacin da Janar Abacha ke mulki, to, don yau na fito na ci gaba da shi zai a ce wani abu. Amma mutane dole su yi adawa a kaina saboda sun san abubuwan da suke yi da ke kawo musu abubuwa cikin aljihunsu, musamman wadanda suka san suna aikata abubuwan da ba su da kyau. Kamar ’yan sanda ne da ke sanya shinge a kan hanya wanda Sufetto Janar ya hana su amma ba su daina ba. Amma in ka hana dole sai an ciza a gyara. Fatata ita ce a gyara domin kasar nan ita kadai muka sani, kuma wanda duk ya ki tashi tsaye domin a gyara Najariya saboda yana shakka ko tsoron za a zage shi ba shirin alheri ya yi ba.
Aminiya: Ganin akwai sarkakiya wajen tafiyar da al’amuran da suka shafi matasa wasu sababbin matakai ne kake dauka domin cimma muradinka?
Al-Mustapha: Matakin farko shi ne matasa a fada musu gaskiyar yadda abubuwa suke kuma a rika neman abokan da suke da zuciyar taimakawa. Yanzu ba ka gan ni da wasu abokan ba to su kansu Allah kadai Ya san abin da suke kashewa a garuruwan da muke zuwa wajen taimaka wa mutane. Idan mun ga kungiyoyin matasa da abin da suke yi da duk zai iya fito da wani abu sai ya yi. Abubuwan da suke yi alhamdulillah haka nake so a dore. An yi wa da yawa, yau akwai wadanda suka zama gwamnoni a cikin harkar kungiyoyi. Duk lokacin da ka ga kungiya ko mutane ko gari, mai kudi yana ganin ba hakki ne a kansa taimaka wa talaka ba, to hadari ne wannan. Ko kuma masu mulki ba za su rika tunanin talaka ba shi ma hadari ne domin su talakawa suka fi yawa. Su kuma suke da hakkin a taimaka musu, kuma dole ne a yi haka domin ba za a ci gaba da tura mutane bango ba domin yin haka zai sa su rika yin bore. Idan kuwa haka ya faru ke nan ba a yin mulki da lissafi ko masu kudi suna zama da marasa shi a kan rashin tausayi da sanin ya kamata.
Aminiya: Wannan fafutika ta hada da Kudancin Najeriya ne ko kuwa Arewa ce kawai?
Al-Mustapha: Ta hada ko’ina domin a Kudancin Najeriya ina da kungiyoyi da dama da na yi abubuwa da su a kan zaman lafiyar Najeriya. A Kudu akwai ’yan Arewa, idan ka yi abota da wani da ke Kudu kuma sai wata ’yar baraka ta auku a tsakaninku shi yana cikin wata kungiya babba kuma aka tashi ana dukan ’yan Arewa ta wacce hanya zaka yi gaggawar magana sai ta kungiyar.
Ba hukuma ce za ta iya yin komai ba, alaka a tsakanin mutane babban abu ne da ita kanta hukumar abin da take son yi ke nan wajen hada kan mutane. Duka muna da hakki, hatta kai mai tambaya kana da hakkin gyara.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya