Kotu ta aike da matashi gidan kaso bisa zargin fyade

Fyade

Wata kotun majistare dake zamanta a Legas ta aike da wani matashi mai suna Taofeek Bakare zuwa gidan kaso bisa zargin yi wa yarinya fyade.

Alkalin kotun, Mai Shari’a F. M. Alamu-Kayode ne ya umarci a tsare matashin mai kimanin shekara 32 a gidan kaso na Ikoyi, har zuwa lokacin da za a kammala bincike a Kotun Yaki da Cin Zarafi.

An dai gurfanar da wanda ake zargin ne bisa zargin lalata yarinya, ko da yake ya musanta aikata laifin.

Dan sanda mai gabatar da kara, Olu Olubiyi ya shaida wa kotun cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne a ranar 13 ga watan Satumba a unguwar Ikorodu.

Ya yi zargin cewa Taofeek ya yi lalata da yarinyar mai kimanin shekaru 17 wacce ya yi ikirarin cewa budurwarsa ce.

A cewar dan sandan, laifin ya saba da sashe na 137 na kundin manyan laifuffuka na jihar Legas wanda ya tanadi hukuncin daurin-rai-da rai ga masu aikata laifin.

Daga nan sai alkalin ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa 10 ga watan Disamba.