✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta b a da belin mutum 7 da ake tuhuma da kisan Janar Alkali

A shekaranjiya Laraba ce Mai shari’a Daniel Longji na Babbar Kotun Jihar Filato, ya bayar da beli ga ragowar mutum 7 da ake tuhuma da…

A shekaranjiya Laraba ce Mai shari’a Daniel Longji na Babbar Kotun Jihar Filato, ya bayar da beli ga ragowar mutum 7 da ake tuhuma da laifin kisan tsohon Kwamandan Al’amuran Gudanarwa na Rundunar Sojin Najeriya, marigayi Manjo Janar Idris Alkali (mai ritaya).

A cikin watan Disamba bara ne, kotun ta bayar da belin mutum 20 da aka tuhuma da hannun wajen kisan marigayin. An tuhumi mutanen ne da laifuffuka biyar da suka hada da hadin baki da kisan kai da kin tona asirin mai laifi da gangami domin aikata laifi da kuma hana jami’an tsaro gudanar da bincike.

Mai shari’a Longji ya bayar da belin mutum bakwai din ne a kan Naira miliyan 5 kowannensu, tare da gabatar da masu tsaya musu, da kowanne zai gabatar da satifiket na mallakar gida ko fili a jihar.

Haka kuma kotun ta gindaya musu sharadin cewa babu wanda zai yi tafiya ya bar Najeriya ba tare da amincewar kotun ba kuma dole ne su rika halartar kotun daga lokaci zuwa lokaci har a kammala shari’ar.